Za A Soma Kama ‘Yan Shi’a Da Shugabaninsu A Nijeriya

0

Za A Fara Kama ‘Yan Shi’a Da Shugabaninsu A Nijeriya

Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa Muhammed Adamu ya ba da wata sanarwa inda yake umurtan kwamishinonin sa na kasa baki daya don fara kame membobi da shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN) wanda Sheikh Zakzaky ke jagoranta da rushe gininsu a fadin jihohi.

A cikin umarni na musamman da oda ga dukkan ‘yan sanda a fadin kasar, IGP ya umarci kwamishinonin’ yan sanda da su dakile dukkan ayyukan kungiyar Harkar Musulunci kai tsaye.

IGP Muhammed Adamu ya zargi membobin kungiyar da gudanar da wasu zanga-zanga da suka saba ka’ida.

Wannan sanarwa na zuwa ne a farkon farkon watan kalandar musulinci, a lokacin da mabiya Shi’a ke kokarin fara gudanar da manyan aikace-aikace da tarukan su na addini.

Leave A Reply

Your email address will not be published.