Tohfa Shugaban Kasa Buhari Yanemi Sulhu Da Y’an Shi’a

5 475

Yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda rikici tsakanin jami’an tsaro da ‘yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim el-Zakzaky ke kara kazanta, wasu bayanai na cewa bangarorin biyu sun “gana da juna domin neman mafita”.
Tun bayan tsare jagoran na kungiyar ‘yan uwa Musulmi tare da matarsa a shekara ta 2015, magoya bayansa ke zanga-zangar ganin an sake shi, inda suke taho-mu-gama da ‘yan sanda, lamarin da kan kai ga hasarar rayuka da dukiyoyi.
Kakakin kungiyar Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa an yi wata “ganawa tsakanin wakilansu da kuma jami’an tsaron farin kaya na DSS” domin lalubo bakin-zaren, amma ba a kai ga cimma wata mastaya ba.
Sai dai ya ce ba zai yi karin bayani kan ainahin abin da aka tattauna ba da kuma batun da ya kawo tsaikon da aka samu, yana mai cewa sirri ne.
BBC ba ta iya tabbatar da wannan ikirari nasa ta wata kafa mai zaman kanta ba.
Batun rikicin na ‘yan Shi’a dai na ci gaba da haifar da zazzafar muhawara tsakanin ‘yan kasar, inda kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke kiraye-kirayen a binciki yadda suka ce ‘yan sanda na yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar, lamarin da suka musanta.
A kalla mutum 13 ne aka kashe a rikici na baya-bayan nan, ciki har da wani dan jarida na gidan talbijin na Channels da wani babban jami’in dan sanda da kuma ‘yan Shi’a 11. Kodayake daga bisani sun ce adadin da aka kashe musu ya haura haka.
Batun tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa gwamnati na duba yiwuwar haramta kungiyar ta ‘yan Shi’a baki daya.
Sai dai masu lura da al’amura irin su Mannir Dan Ali, shugaban kamfanin jaridar Daily Trust na ganin beken haramta kungiyar inda ya ce “ba ya tsammanin haramta kungiyar ta IMN zai samar da zaman lafiya sai dai ma ya kara ta’azzara yanayin tsaro.”
Ya kara da cewa “hanyar da ya kamata gwamnati ta bi wajen warware al’amarin ita ce ta bin umarnin kotu.”
Sai dai ya bai wa gwamnatin shawara cewa “idan gwamnati ta bi umarnin kotu ta saki Elzakzaky tana da karfin ikon da za ta iya masa daurin talala domin takaita zurga-zurgarsa.”
Tun a shekarar 2015 ne ake tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da jami’an tsaro suka kai wa magoya bayansa a Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 300.
Tun lokacin ne kuma mabiyansa ke ta zanga-zangar neman a sako shi, suna masu zargin cewa “yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya”.
Lamarin da yake kuma kaisu ga yin taho-mu-gama da jami’an tsaro akai-akai wanda ke haifar da hasarar rayuka da ta dukiyoyi.
Ko a farkon watannan sai da suka kutsa kai majalisar dokokin kasar domin neman ta sa baki a saki shugaban nasu, lamarin da ya kai dage zaman majalisar da kuma harbe wasu magoya bayansu.