Ta Hadu Da Sharrin Kafofin Sada zumunta (Social media) Hotuna

1

Wannan yarinya sunanta Sadiya daga garin Jos jihar Pilato, ana cikiyarta, ta bata bat yau wajen kwana biyar

Ta hadu da wani mutum da suka hadu a dandalin sada zumunta, ya mata alkawari zai zo Jos su gana, ta fita daga gidansu akan zata taro bakon nata, to tun daga wannan lokacin ba’a sake jin duriyarta ba

Kuma tun daga lokacin fitar ta daga gida zata taro bakonta nambar wayoyinta duk a kashe, an nemeta sama da kasa an rasa, kuma ba’a san ta inda suka hadu da mutumin ba balle a fara bincike
A yanzu dai ‘yan uwanta sun fitar da neman cikiyarta, jama’a sai a taimaka ko da addu’ah

Daga bangarenmu zamu hada ‘yan uwanta da masu bincike a wannan fanni Insha Allah

Bayan haka ‘yan uwa ayi taka tsantsan, wannan darasi ne garemu gaba daya, a guji saurin yadda da mutane musamman wadanda aka hadu ta kafofin sada zumunta

Muna rokon Allah Ya bayyanata cikin aminci Amin

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

1 Comment
  1. E.o says

    Allah yasa agane ta.