SAKACI Part 23

1
Aikuwa da safe da ta bud’e fridge d’in ba farfesu ba alamarsa, tasan ba kowa ne ya d’auka ba sai Dr.
Toh kuma ita ai har zuwan wannan lokacin bata bud’e kofa ba, toh ta yaya ya shigo har ya d’auka.
“yana da wani key ne a hannunshi” zuciyarta ta ba ta ansa, haka ta cigaba da aikace-aikacents da mamakin Dr fal cikin zuciyarta.
Tun daga wannan ranar Dr bai sake yarda sun had’u ba, sai dai ya tura ma ta sak’o ta waya ya tambayeta lafiyarta.
Idan kuwa ranar girkinta ne, toh nan fa zai shiga kitchen ya samawa kansa abin ta6awa.
Lura da ta yi yana zuwa cin abincin cikin dare bayan ta
kwanta yasa ita kuma ta dage da dafa duk wani abinci da ta tabbatar yana
so, ta ajiye mai.
                   ****
Yau ne hutun ta ya k’are, don haka murna ta keyi sosai, dama ta gaji da zaman wuri d’aya, ko ba komai yau zata samu canjin wuri.
Ta sha mamaki lokacin da Dr ya tura mata sak’o ta waya yana tambayarta k’arfe nawa zata tafi aiki, domin ta yi tunanin ya manta.
Karfe takwas ya turo da driver yazo ya d’auke ta.
Farida mace ce da kowa yake sonta saboda kyawun halayenta,
da son mutane gami da kyauta, shiyasa duk inda ta shiga a fad’in
asibitin nan ake martabata da bata girma.
                    ****
Ta na daf da shiga ICU ta hangota, cike da farinciki Dr Jidda ta k’araso wurinta, rumgume juna sukayi cikin kewa.
Dr Jidda ce ta saketa gami da d’an ja baya kad’an, rike baki ta yi alamar mamaki kafin kuma ta ce.
“Kawata kinganki yadda kikayi fresh kuwa, fatarki sai wani
shek’i ta keyi, gaskiya aure ya k’ar6eki kawata kuma da alama ubangidan
nawa ya iya kiyo”
Ta6e baki Farida ta yi gami da cewa “nifa banga wani dad’i a wannan auren ba Jidda”
“Wai kina nufin Dr har yanzu bai bada kai ba” Jidda ta fad’a.
” Hmm, idan ya ta6a kwana d’aki d’aya dani kenan, nifa…..”
Ganinshi a gabansu yasa maganar ta tsaya a mak’oshints ba
ta re da ta iya k’arasawa ba, cikin k’ank’anin lokaci ta shiga rud’ani.
Bai sa ke kallon inda suke ba, yayi wucewarshi, cikinsu ba wacce ta iya magana, sai daga bisani ne Jidda ta ce.
“Alllah dai yasa bai ji abinda muke fad’a ba”
“Ma had’u anjima Jidda” abinda Farida ta iya fad’a kenan, kafin kuma suyiwa juna sallama ko wacce ta kama gabanta.
                   ****
Yau gaba d’aya ta yi wuninta ne cikin fargaba, ganin har
lokacin tashi daga aikinta yayi har wannan lokacin bata samu kiran Dr ba
yasa hankalinta ya d’an kwanta, kad’an.
Indomie ne a gabanta ta naci lokaci zuwa lokaci hankalinta
yana kan film d’in da ta ke kallon a TV, Sallama yayi had’e da shugowa,
kasancewar hankalinta na kan film d’in da ta ke kallo yasa bata ji
sallamar da yayi ba, balle kuma ta san da shigowar shi.
Gyaran muryarshi ce ta ankarar da ita, a ta ke zuciyarta ta
bada ras, lokaci guda kuwa ta tsahi tsaye cikin fargaba, wani kallo ya
ke jifanta da shi, kallo ne wanda ta riga tasan na 6acin rai ne.
Lokaci guda fargabanta ya dad’u fiye da baya, k’arasawa yayi ya zauna akan kujera.
Cikin yanayi na 6acin rai ya ce “ai bansan rashin
mutuncinki ya zarce tunanina ba, ban kuma san cewa Islamiyar da najima
ina kaiki na dawo dake duk runtsi bana miki wasa da ita ashe duk abanza
ne, babu abinda kike fahimta”
Wani irin murd’awa cikinta yayi har saida taji tamkar gudawa zai fito, “magana nake miki” ya fad’a cikin tsawa.
Sunkuyar da kanta ta yi ba tare da ta tanka mai ba.
” Na gode kinje kin tona min asiri awaje, tunda ke baki san laifin tona sirrin aure ba”
“Ba ma haka ba, ke don Allah ba abin kunya ba ne a gareki
ace auren fari amma kinje kina fad’awa jama’a mijinki ba ya had’a gado
da ke”
“Wallahi ban ta6a ganin jarababbiyar mace irinki ba, wacce ba kunya a idanunta”
Ya cigaba da cewa.
“Toh inaso ki bud’e kunnuwanki kiji ni da kyau, bazan ta6a
iya had’a jiki da ke ba, ko kina tunanin zan manta da irin kazantar da
kuka aikata ke da wancan kazamin da kika gama cimun mutunci akanshi ne”
“Allah ya sauwak’a, turrr da halinki wallahi”
Wani kuka mai zafi ta fashe da shi, cikin wani irin yanayi Farida ta ce! 
“mai yasa ka aureni”
Cike da masifa ya ce “shak’eni sai na baki ansa, kuma zan
miki gargad’i idan kin d’auka kinsamawa kanki lafiya, wallahi kika sake
zuwa kika bud’e min sirrin gidana a waje, saina nuna miki other side of
me”
Ya na gama fad’an haka yasa kanshi yayi ficewarshi, kwanciya Farida ta yi ta na kuka mai ban tausayi gami da cewa.
Mama aure bai kar6emu ba, nima kinga yadda rayuwata ta
dawo, duniyar ta yimin zafi Mama, nima nasan nakusan zuwa gareki, Ya
Umar ba masoyinmu ba ne, Mama ya yaudaremu ne”
Kuka sosai ta keyi ta cigaba da surutai tamkar wacce ta zare.
Yana tsaye a k’ofar falonta ya na sauraran maganganunta,
wani irin zafi zuciyarshi ta keyi, ya rasa dalilin da yasa ya kasa manta
laifin da Faridanshi ta aikata mai.
Dukan bakinshi ya ke da hannunshi ya na cewa “banyi ba mai
yasa na kasance mai k’untatawa wacce nafi so fiye da rayuwata, why why?”
Juyawa yayi da nufin yaje ya rungumeta ya rarrasheta, amma
lokaci guda hoton ta ya hango ta na rungume a jikin Adamu, a take
zuciyarshi ta yi mai zafi, juyawa yayi gami da tafiya shashinsa.
Ko da ya koma shashinsa rasa abinda yake mai dad’i yayi,
wani irin tausayinta ya keji, mafita yake nema amma sam k’wak’alwarshi
ta kasa hasko mai komai.
Yana bukatar ya mance wannan rana daga cikin tarihin
rayuwarsu amma ya kasa, to wai shi ya zai yi ne, wa zai tunkara ”
*ALLAH* ” zuciyarshi ta bashi ansa.
Toilet ya shiga gami da d’auro alwala, sai dai lokacin da
ya idar da sallah sai ya rasa wace addu’a zaiyi me ma zai rok’i Allah,
komai ya tsaya mai, k’arshe hakura kawai yayi.
                     ***   ***
Farida ma kwana ta yi ta na kuka gami da yiwa mutumin da ya
6ata ma ta rayuwarta Allah ya isa, domin tasan da badan hakan ba, ba
wani namijin da ya isa ya zageta, tabbas wata shari’ar sai a lahira.

Ranar dai duk cikinsu ba wanda ya runtsa har sai bayan sallar asuba.

Kasancewar bai kwanta da wuri ba yasa ya makara, d’akin
Mariya ya soma shiga, bai sameta a falo ba, jiyo hayaniyar Muhammad
(d’ansu na uku) a kitchen hakan ya tabbatar mai da suna kitchen d’in.
Don haka kai tsaye kitchen d’in ya nufa, da gudu Muhammad
ya zo ya rungume Babanshi, d’aukanshi Dr yayi yana mai wasa, kafin kuma
ya juyo ga Mariya wacce ko kallo bai isheta ba.
Ya lura tunda ya auri Farida sam ya rasa kulawa a wajen Mariya, ita kullun gani ta ke yana fifita Farida akanta.
“Ranki shidad’e baki ji shugowata bane” Dr ya fad’a, ta6e
baki ta yi had’e da cewa ” ai gani na yi maganar tawa bata fiye zama mai
anfani ba, tunda kullun gani ake inada k’orafi, k’iri-k’iri za’a cuceni
ace kuma kar na yi magana”
Murmushi yayi gami da cewa “Hajiya Mariya kenan to yau ma na yi lefi ne”
“Dr ka maidani yarinya karama, duba agogo k’arfe goma kana
d’akin ta gaban goshin taka, ba labarin office, balle kuma mu musami
darajar azo aduba lafiyarmu, su khalil har suka tafi school basu sami
ganinka ba”
“Yi hakuri bank’i zuwa dubaku da gan-gan ba, ni kaina makara na yi” Dr ya fad’a, 
Ciki fad’a Mariya ta ce ” Ai ba sai ka fad’amin kwana
kukayi bakuyi bacci ba, nasan da haka, kuma cutar da akeyimin Allah na
gani”
Ganin idan ya tsaya ranshi ne zai 6aci yasa ya kama hannun d’anshi suka yi tafiyarsu ya barta ta nata sababi.
Kai tsaye shashin Farida ya nufa domin yana buk’atar
ganinta hankalinshi sam yak’i kwanciya, sanin da yayi jiya ya barta
cikin halin damuwa.
Goge kujerunta ta keyi, suka shigo, Muhammad ne yazo gareta cikin sakewan fuska ta rungumeshi ta na “oyoyo Alhajina”.
So yake ya had’a ido da ita amma sam tak’i yarda, kallonta
ya ke sosai tabbas ta bashi tausayi duk da bata bata bari ya kalli cikin
idonta ba.
Amma idanunta sun kumbura wanda yasan ba tantama kwana ta yi tana kuka.
“Ina kwana” ta katse mai tunani ba ta re da ta kalleshi ba,
cikin sanyi muryar da ya bata mamaki ya ansa, sannan ya ce “kintashi
lafiya”
Tambayar da ya mata yafi mata kama da ta rainin hankali, domin haka bata ansa ba.
Ya d’auki lokaci mai tsayi yana zaune a wurin har taje ta
had’awa Muhammad tea ta dawo bai motsa ba, abun sai ya mata wani irin,
domin bai ta6a kwatanta hakan ba.
“Ki shirya ranar juma’a zamuje Jos mu gaishe su” ya katse mata tunani, gyad’a kai ta yi, alamar ” toh”
Sai da ya tashi tsaye kafin ya ce “Alhaji na barka wurin Mamanka zaka taya ta hira ko” yaro ya gyad’a kai alamr ” eh “
Ranar haka suka wuni da Muhammad, tabbas yaron ya d’ebe mata kewa.
Ita kuwa Mariya ba ta yi tunanin gun Farida Dr ya kai
Muhammad ba, ta yi zaton suna ta re ne, da tana da masaniya da tuni tazo
ta d’auke d’anta.
Sai da yamma da yaji hayaniyar y’an uwanshi suna wasa awaje, ya fita ya, daganan ne bai sa ke dawowa ba.
                       *****
Da wuri ta kammala shirinta ta na fargabar zuwa Jos d’in amma kuma ta na son taje ta ga Ummi.
Sanin Dr ya siyawa su Ummi gida a unguwar Ibrahim tayo,
yasa fargabanta ya ragu, domin ba taso ta kuma lek’a unguwar da al’amura
da dama suka faru acikinta.
Anayin sallah juma’a Dr ya umarcesu da su fito, Mariya dai gudun 6acin ranshi ne kawai yasa zata je amma bawai don tana so ba.
Ita a tunaninta salon a wulak’anta ta ne kawai yasa aka tsiro da tafiyar da ita.
Koda suka fito da saurinta ta wuce Farida harda bangajeta ta shiga gidan gaba, azuciyar Farida ta ce
“Hmm ke gaba ya dama da kinyi hakuri ma ni ba shiga zanyi ba”
Tafiyar kurame sukayi a motar ba wani mai magana d’an gara Farida ta biyewa yara suna ta ma ta surutunsu na yara.
                ****
Da gudu taje ta rungume Ummi, cike da farinciki Ummi ta ce “oh ni wai Farida Umar sai kin k’arasa ni”
“An zo wurin” Mariya ta fad’a a zuciyarta, yak’en dole kawai ta keyi amma ba karamin haushi sunan ya ke bata ba.
Sosai Ummi ta ke farinciki, duk motsin da Farida zata yi idanunn Ummi na kanta.
Cikin k’ank’anin lokaci aka wadatasu da kayan ciye-ciye da
na sha, sai da sukaci sukayi dam kafin suka tashi suka gabatar da sallah
la’asar.
Mariya ce ta ce “na fito ne ka saukeni a gidan Auntyn tawa” ta fad’a lokacin da ta ga yana shirin fita.
Fuska  ba walwala Dr ya ce “sai da daddare “
“Don girman Allah ka kaini yanzu” zaiyi magana Ummi ta katseshi da ce wa
“A’a tunda ta had’aka da girman Allah ka kai ta”
Ba zai iya musu da Ummi ba yasa ya kad’a kai kawai gami da
ce wa “ba da yarana za kije ba” “toh” kawai ta ce domin tasan dole akayi
mai bawai don yana so ba.
Bayan sun tafi yara kuma ansa musu kallo, Ummi ta kamo
hannun Farida gami da ce wa ” d’iyata me yake damunki ne, dubi yadda
kika rame”
Murmushi Farida ta yi kafin kuma ta ce “me kika gani Ummi ba fa komai, ni ba abinda yake damuna”
Ummi ta ce “Farida kalli cikin idona ni ba yarinya bace a
gabana aka haifeki don haka babu abinda za ki boye min, idan har kin
d’aukeni a matsayin uwa Farida ki sanar dani abinda ya ke damunki”
Hawayen da ta ke mak’alewa ne ya fara zubowa, cikin muryar kuka Farida ta ce “Ummi ki raba auren nan please”
Murya mai cike da damuwa Ummi ta ce “wani abu yayan naki yake yimiki, sanar dani Farida karki 6oyemin komai”
“Ummi ba komai nidai ki taimaka ki sakashi ya sakeni idan ba haka ba wallahi ciwon zuciya nima shi zai zama ajilina kamar Mama”
Rungumeta Ummi ta yi gami da cewa ” shi d’in waye wallahi
bai isa ya wukantaki ba, bai isa ba wallahi dani ya ke, kwantar da
hankalinki Faridana wallahi Umar bai isa ba, ni zanyi magani komai, ki
manta dashi kinji, karna sa ke jin batun ciwon zuciyar nan”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

1 Comment
  1. Anonymous says

    Your Comment sure sirri