SAKACI Part 22

0

A tsaye ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai safar
da marwa ya ke  a cikin office d’in, fuskarnan a murtuke, gaggawan sauke
idanunta ta yi saboda wani kallo da ya ke jifanta da shi.

A ta ke zuciyarta ta fara bugawa da sauri-sauri, rawa jikinta yake tamkar mazari.
“Mene ne hujjarki ta zuwa ki zauna a tsakiyar wa’encan garadan”
Ba ta iya d’agowa ta kalleshi ba, bare kuma ta bashi ansa,
“magana na ke miki” ya daka ma ta tsawar da har sai da taji ta har
tsakiyar kanta.
Ba ta iya d’aga kanta ba ma balle ta ba shi ansa, cikin maganarshi ta k’asaita ya ce!
“Kinyi na farko sannan kinyi na k’arshe, ya kamata ace
kinsan ke matar aure ce, ni kuma da kika ganni nan ba sakaren namiji ba
ne, don haka idan kika sa ke mai-maita makamancin hakan, ke da aiki sai
dai kiga anayi, da fatan kin fahimci abinda na ke nufi”
“Kayi hakuri, hakan ba zai sa ke faruwa ba” ta ce da shi,
har cikin ranshi ta bashi tausayi, amma tunowa da abinda ya hana
zuciyarshi sakat yasa shi shiga wani irin yanayi, lokaci guda kuma
zuciyarshi ta yi bak’i.
Idan ba darajar iyaye ba yaushe hakan zai faru, Allah ya
gani bai ta6a aikata zina ba, yana mugun kyamarta, sannan bai ta6a
gajiyawa ba wurin rok’on Allah akan ya had’ashi da salihar mace.
“Kai Farida kin cuceni na jima ina inganta rayuwarki lokaci
guda ki wargaza komai, mai wannan yaron ya rud’eki a wannan lokacin
kika bashi kanki”
Ko zan hana kaina abu ke zan baki kawai don bana so wani ya sake rud’anki a karo na biyu, amma kin rusa min komai.
Kujera ya samu ya zauna ya fuzar wata iska mai zafi daga cikin bakinshi.
“Ki zauna na kammala wani aiki kafin mu shiga tiyatan” Ya fad’a ya na janyo jakar laptop d’inshi.
Zama ta yi gami da takurewa wuri d’aya domi ita sam yanzu ba ta sa kewa muddin yana wuri.
Ya kai kusan awa guda (1hr) kafin ya umarceta da su tashi su je dan gudanar da aikin da ke gabansu.
 
                     ****
Basu suka bar asibitin ba sai karfe sha biyu (12) na dare,
Mariya ta cika ta yi fal, saboda a ranar ta kar6i girki, sannan ta ga
fitar Farida da ga gida, don haka ta kasa tsaye ta kasa zaune, zuciyarta
fal kishi.
“Don Allah AC bedroom d’ina da na falo ba sa yi ga zafi, ko zaka taimaka ka dubamin” Farida ta fad’a cikin sanyi muryarta.
“Tun yaushe ne ya daina yi” ya tambaye ta.
“Dama tunda nazo gidan bai ta6a yi ba” ta ansa mai, tsaki ya ja gami da cewa, 
“Amma kullun ina tambayarki inda wata matsalar sai kice babu”
Ita dai ba ta ce komai ba, bud’e murfin k’ofar yayi yana
shirin fita, ita d’inma fitar ta yi, ta na aiyana irin zafin da zata sha
yau, domin zafin yau yafi na kullun.
Ga mamakinta taji ya na binta a baya, ko ba komai taji dad’i.
Ta na tsaye ta na kallon ikon Allah, ranta bai gama 6aci ba
sai da taga ya na bin Farida shashinta, tabbas tasan tunda Farida ta
shigo gidan k’arshenta yazo, ba ta shigo bama sai da ta kusa korarta, eh
toh korarta mana.
Sam basu lura da ta wurin ba, koda suka shiga kai tsaye
d’akin baccinta ta bud’e mai ya shiga, wata y’ar stool ta mik’o mai akan
ya hau kai.
“Wannan sai marasa tsayi irin ku” ji ta yi tamkar a
mafarki, idan kuwa ba mafarki ba ne, toh babu tantama kunnenta baiji ma
ta dai-dai ba.
“Wai tunanin me kike ina miki magana hankalinki baya nan”
ya fad’a da muryar da baza ta iya tantance wa da fad’a yayi maganar ko
akasinta ba.
“Banji mai ka ce bane” kafin ya kai ga magana sukaji ta banko k’ofar, lokaci guda suka kalleta.
“Toh maciya amana ranar kwanan nawa ma sai anci amanata ko
tsoron Allah bakyaji, toh wallahi na gaji da ganin bakin ciki, a cuceni a
hanani kuka ba zai yuwu ba”
“Ba ta re da ya tanka ma ta ba ya ratsa ta gefenta yayi ficewarshi, tabbas ta kula, kuma ta san hakan gargad’ine ya ma ta.
Juyowa wurin Farida ta yi hannunta a k’ugun  kafin kuma ta
ce ” wallahi dani kikeyi na miki alkhawarin sai kin fita kinbar gidan
nan, zanje na sa meshi sai dai ya za6a tsakanin ni da ke, munafuka”
Daga haka ta fice, Farida ko kallo Mariya bata isheta ba,
ita tasan ko giyar wake Mariya tasha baza ta tunkari Dr da wannan
maganar ba, idan kuwa ta yi gangancin fad’a zai bata mamaki, domin shi
ba’a mai gatse.
               ****    ****
Washegari da safe ya shigo lokacin ta yi wanka har ta gama gyaran gidan, ta shiga kitchen ta na had’a tea.
A tsaye ta sameshi sanye cikin light brown d’in riga mai
gajeren hannu, wandon kuma dark brown, kalar kayan sun kar6eshi matuk’a,
kasancewar kalar fatarshi ne.
Sumar kanshi a gyare, ya kwanta luf gwanin sha’awa, kai gayen ya had’u ta ko’ina.
Idan ka kalleshi za ka d’auka matashi ne d’an shekara talatin, ba zaka ta6a cewa ya kai shekara arba’in da biyar ba.
Dr akwai iya d’aukan wanka, kuma duk kayan da ya saka zaka ga ya k’ar6e shi.
Sannan shi mutun ne mai tsafta shi yasa kafin ka ganshi k’amshin shi ne zai fara yimaka sallama.
Tsugunawa ta yi gami da gaisheshi, ansawa yayi fuskar nan kamar ko yaushe.
“AC jiya yayi” ya tambaya a tak’aice “eh yayi” ta bashi ansa, kafin ya sa ke cewa,
“Ni zan fita ki shirya anjima zanzo na d’auke ki”  “toh, Allah ya tsare” ta fad’a, “ba wani abunda kike buk’ata”
Ya sake tambayarta, da sanyin murya ta ce ” eh babu” ta ansa.
Juyawa yayi yana wannan tafiyar nan tashi.

Zama ta yi ta rasa me ya ke ma ta dad’i a rayuwa, sam ba ta
kaunar wannan hali na ko inkula da yayanta yake nuna ma ta, k’arshe tea
d’in da bata sha ba kenan

Yau ne Farida ta kar6a girki kuma yau ta na da niyar ta
kyautatawa yayan nata shiyasa ta wuni gyaran gida, duk da gidan ba wani
datti ne dashi ba, amma sanin halin yayan nata da son tsafta yasa ta yi
k’ok’arin kimtsa komai.
Ta na gama gyaran gida ta hau na jiki duk ba ta da tabbacin
wanda ta keyi dominsa zai yaba, amma dai a ganinta bai kamata wannan ya
zama hujjarta na k’in gyarawan ba.
Shiga kitchen ta yi, ta na tunanin mai za ta dafa mai wanda
tasan zai yaba, tunowa da ta yi a rayuwar Dr yana son shinkafa da wake
da kuma miya, ko bayason cin abinci aka bashi wannan zai ci sosai.
Sannan kuma mutun ne mai son farfesun kayan ciki, ba tare
da 6ata lokaci ba ta nemi Isiyaku mai sharan gida da gyaran flawa, ta
aikeshi kasuwa ya siyo mata duk abinda ta ke bukata.
Cikin k’ank’anin lokaci gidan ya kaure da k’amshi, daf da magriba ta kammala komai gami da jerasu akan dining table.
Wanka ta shiga, gami da d’auro alwala, ta fito dai-dai an
kira sallah don haka kayan da ta ke sallah da shi ta zira had’e da
shinfid’a sallaya.
Ko da ta idar da sallah ba ta tashi ba azkar ta cigaba da yi kafin lokacin sallah isha’i ta tashi ta gabatar.
Kwalliya ta yi, wanda rabonta da ta yi irinshi ta manta,
tabbas ta san ta yi kyau, material ta d’auko mara nauyi, kasancewar
garin akwai zafi.
Doguwar rigace d’inkin fitet, ya kamata sosai dama gata masha Allah, ko’ina ya fito ba’a magana.
Kasancewar ita masoyiyar turare ne yasa ta fesa kusan kala
shida ajikinta, gasu masu sanyin k’amshi shi d’in ne kuma ya bada
k’amshi mai sanyi ga dad’i.
Kama gashinta ta yi da ribon kafin kuma ta kafa d’auri wanda ya mata kyau matuk’a.
Falo ta fita, zama ta yi akan kujera ta zaman mutun d’aya kafin kuma ta janyo wayarta, Ummi ta kira.
Cikin farin ciki suka gaisa da Ummi, Ummi ta ce “Farida Umar kinsamu
Yayanki kin manta dani ko”
Cike da shagwa6a Farida ta ce “ni na isa na manta da
Ummina” Ummi ta ce “toh ba lefi da fatan dai kuna lafiya, ba wata
matsala ko?”.
Farida ta ce “ba komai Ummina sai kewarki” murmushi Ummi ta
yi irin nasu na manya kafin kuma ta ce “karki damu d’iyata da nasamu
saukin aiki zanzo naganki”
Ummi ta sa ke cewa “yauwa kafin na manta, kina yawan yin wannan addu’o’in da na baki”
Farida ta ce ” wanne daga ciki Ummi” Ummi ta ce ” wanda na
ce ki dinga yin Istigifari, Salatin annabi da Lahaula wala k’uwata illah
billah, na fad’a miki duk wanda ya lazimcesu ba adadi insha Allahu
zaiga biyan buk’ata aduk abinda ya sa gaba, don haka ki dage kinji”
Farida ta ce “toh Ummi inayi amma zan k’ara dagewa, Allah ya k’ara girma Ummi”
“Ameen” Ummi ta ce da ga nan sukayi sallama gami da ajiye waya.
Dai-dai wannan lokacin ya shigo, hannuwanshi cikin ajjihun wandonshi, kallonta ya ke baya ko k’ifta ido.
“jibi mutumin nan inda ya samin ido, yanzu da ni ce na ke
mai irin wannan kallon da kaji bak’ak’en maganganu” ta fad’a a
zuciyarta.
Shima maganar ya ke a zuciyarshi “Wow, Allah na gode maka da ka azurtani da wannan zankad’ed’iyar matar”
“Sannu da dawowa” ta katse mai tunani, cikin basarwa ya ce
“ke me yasa baki san kalar kwalliyar da tafi dacewa da zamani bane, haba
abu sam ba fasali ya kamata kisan irin kwalliyar da za ta miki kyau,
mtsss” ya karashe da jan tsaki.
Shi kanshi yasan abinda ya fad’a ba gaskiya bane, amma gudun karta yi tunanin ta burgeshi yasa yayi haka.
Wani bakin ciki ne ya tokare ma ta mak’oshi, cikin sanyin murya ta ce “na kawo maka abinci ne”
Fitanshi yayi ba tare da ya tanka ma ta ba, ba kuma don baya jin yunwa bane sai kawai don tsare gida irin nashi.
Yau kam ma ta gagara yin kukan saboda bakin ciki, Qur’anin ta ta d’auko domin ta na bukatar abinda zai sanyaya ma ta zuciya.
Ba ta ajiye Qur’anin ba sai da ta ji ta samu sanyi a cikin
zuciyarta, abinci ta d’iba dai-dai wanda za taci sauran ta zuba a babban
wormer, hijab d’inta ta zura gami da fita.
Mai gadi taje ta bawa abincin, da murnarshi  ya kar6a,
bud’ewa yayi yana kallo gami da saka ma ta albarka, juyawa ta yi domin
tafiya dai-dai wannan lokacin ya shigo gidan.
“Malam musa don Allah zo ka siyomin biredi” idanunshi ne ya kai kan abincin, atake yaji yawunsa ya tsinke.
“Malam Musa a ina ka siyo wannan abincin” ya jefa mai tambayar, kasancewar bai lura da ita ba yasa bai gane ita ta kawo ba.
“Alhaji ai yanzun nan dakta ta kawo mana” ya fad’a yana washe baki.
“yaufa za’ayita” ya fad’a acikin zuciyarshi.
“Aikuwa Malam Musa zan maka kwad’ayi domin tare zamuci, ban
san abinda aka dafa ba kenan, na ce na k’oshi na san kuma babu saura a
cikin gidan”
Ya fad’a yana shirin zama akan bencin da Malam Musa yake kai, Malam Musa ya ce,
“Toh Alhaji ai ba komai ni,zubamin nawa ma a murfin kawai” ya fad’a yana yaba irin kyawun halin mai gidan nashi.
Dr ya ce “a’a tare zamuci” “toh ayi haka” Malam Musa ya fad’a cikin farinciki,
Suna cikin ci ta dawo da kwanon farfesu a hannunta, ganin
Dr ya na cin abinci da mai gadi abun ya bata dariya kuma da ta mai tayin
abincin fa ko kulata baiyi ba, gimtse dariyarta ta yi.
Shikuwa kicin-kicin yayi da fuska ya ma cigaba da cin abincin sa tamkar bai ganta ba.
Itama sharewa ta yi sannan ta ce “Malam Musa ga farfesun kayan ciki nan idan zaka k’ara”
Malam Musa ya ce “ayya dakta kinga ni bana cin kayan ciki wallahi”
“Toh ka ajiye idan kaga almajirai sai ka basu” ta fad’a.
“Hoh yarinyar nan za ta kasheni wai sai ta sa naji kunya” ya fad’a a zuciyarshi.
“Kije ki ajiye a fridge zai yi anfani ko zuwa gobe ne” ya
fad’a fuska a murtuke, ita abun ma dariya ya bata, juyawa ta yi cikin
gida ta na dariya ciki-ciki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.