Ra’ayi Riga: Menene Ra’ayin mutane akan rikicin Sarki Sunusi Da Ganduje.

0

Wannan Shiri na ra’ayi Riga zai kawo maku ra’ayin al’ummar Nigeria akan abinda masana Ke kallon rikicine tsakanin sarkin kano Muhammad Sunusi Na Biyu, Da kuma Gamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

A watannin bayane dakta Abdullahi umar ganduje ya kirkiri sabbin masarautu har guda hudu yayinda suka zama biyar kenan sarakunan jihar harda Sarki Sunusi.

A baya dai kotu ta soke nadin saboda karar Da masu Nada sarki a jihar suka shigar amma daga bisani kotu taba gwamnan damar kirkirar sabbin masarautun Sannan kotun tabbatar Da dokar nan Da taba gwamnan damar cirewa Ko Nada sarki aduk lokacin Da yaso.

Saidai dayawa daga al’ummar kasar kowa na fadin ra’ayinsu kamar haka.

1.Wasu Naganin Kirkirar masarautun wani cigaba Ne ajihar.

2.Wasu Naganin Gwamnan yayi hakanne Don nuna ramuwar gayya ga sarkin saboda yadda sarkin bai goyi bayan gwamnan ba alokacin zaben jihar na 2019.

3.Wasu dayawa daga al’ummar kasar suna nuna rashin goyon bayansu ga nadin.

Sannan wasu na ganin gwamnan ya rusa tarihin masarautar wanda yakai kimanin shekaru 1000 .

Leave A Reply

Your email address will not be published.