Ozil, Hazard, Arnautovic, Higuain, Morata, Gueye – Labarin Wasannin Yau

0 36

Coach din Arsenal zai iya barin dan wasa Ozil domin ya bar kungiyar, dan wasan dai yafi kowa karbar albashi a Arsenal din.

Chelsea zasu bukaci a basu kudi kamar Pounds Million 100 akan dan wasansu Hazard idan dan wasan ya nuna sha’awarsa na barin kungiyar.

Dan wasan Tottenham wato Kane ka iya yin jinyar wata 1 kafin ya dawo daga ciwon daya tafi a wasansu da Manchester United.

Sakamakon ciwaon da Harry Kane ya samu Tottenham zata iya karbar aron dan wasan Barcelona mai suna Malcom.

Dan wassan gaba na West Ham wato Marko Arnautovic ka iya komawa kungiyar kwallon kafa ta Shanghai SIPG dake China.

Savilla sunce asun hakura da daukan dan wasan Chelsea wato Morata saboda cewar wai dan wasan yayi musu tsada – sun bada Euro Million 40 an dawo musu da ita.

Sakamakon haka Morata zai rage kudin da ake biyansa ya koma Atletico Madrid – amma Atletico Madrid din kuma dole sai sun sayar da wani daga cikin yan wasansu.

Golan Manchester United yace zai cigaba da zama a kungiyar amma yana bukatar Man United din su kara masa albaashinsa zuwa 300,000 Pound a sati.

Yawa-yawan yan wasan Manchester United suna son Solskjaer yaci gaba da zama coach din kungiyar da din-din-din.

Chelsea sun kammala yarjejeniya da dan wasan Zenith dan Argentina mai suna Leandro dan shekara 24.

Liverpool, Tottenham, da Everton suna neman dan wasan gefe na kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge dake Belguim mai suna Danjuma.

PSG suna neman dan wasan tsakiya mai buga lamba 4, kuma sunce suna son dankan dan wasan Everton dan asalin kasar Senegal mai suna Idrissa.

7
Dan wasan tsakiya na Ajax mai suna De Jong yana daf da komawa PSG akan kudi Pounds Millions 67.