Na Rasa Meyasa Rayuwar Shirin Fim Dina Ta Lalace – Zainab Indomie

3 464

Na Rasa Meyasa Rayuwar Shirin Fim Dina Ta Lalace – Zainab Indomie

Fitacciyar jarumar da aka daina yayinta, Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa ba ta san yaya aka yi rayuwar aktin dinta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a masana’antar fina-finan Hausa.

Jarumar ta ce ta samu daukaka tun tana karama, amma saboda kaddara ba ta san abin da ya faru ba yanzu ta rasa komai.

Ta ce, “Na samu daukaka tuna ina karama, wani abu ya faru yanzu dai na rasa komai, babu ganganci a ciki, ba na kuma ganin laifin kowa, ban kuma zargi kowa ba sakamakon mawuyacin halin da na shiga.

“A halin da ake ciki ba zan iya tunawa da komai ba, ba zan iya cewa ga abin da ya sa na samu kaina a cikin mawuyacin hali ba. Idan har laifina ne ina rokon Allah Ya yafe mini, idan ma laifin wani ne to Allah Ya yafe masa,” inji ta.

Jarumar ta kuma roki Allah Ya sanya ta da sauran jama’a a kan hanya madaidaiciya.

Ta ce, “Na gode wa Allah saboda jarrabawar da ya yi mini, ina rokon Allah Ya fitar da ni daga wannan jarrabawar.

Na mika kaina ga hannun Ubangiji

inji fadar ta