Ma’aikata 3 da ba zasu amfana da karin albashin dubu 30 ba

0 219

Ma’aikata 3 da ba zasu amfana da karin albashin dubu 30 ba

Bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sakawa dokar karin albashi zuwa dubu 30 hannu a jiya, Alhamis,

hadiminshi ya bayyana ma’aikata 3 da baza su amfana da karin albashin ba. Da yake hira da manema labarai,

Sanata Ita Enang wanda shine me baiwa shugaba Buharin shawara akan harkokin majalisar Dattawa,

ya bayyana cewa ma’aikatan da karin albashin ba zai shafa ba sune,

wanda suke aiki karkashin ma’aikatar da ke da ma’aikata da yawansu be kai 25 da wanda ke aikin da kamfanin sufurin jirgin ruwa dake shiga yankin da wannan dokar ba zata yi aiki ba, misali kasar waje,

da kuma wanda ke aiki a karkashin wani aiki na musamman.