Higuain, Eriksen, Koulibaly, Icardi, Modric – Labarin Cinikayyar Yan Wasa

0 50

Chelsea tana dab da daukan dan wasan gaba na AC Milan wato Higuain.

Shuganan Chelsea Abramovic yace Icardi shine wanda yafiso Chelsea su dauka a January.

Inter Milan zata sayar da Perisic don samun kudin sayen dan wasan Real Madrid wato Modric.

Tottenham sunce duk wanda zai sayi dan wasa Erikson sai ya bada kudin daya kai Pounds Million 225.

Dan wasan gaba na Tottenham mai suna Llorenti zai iya komawa Atletico Bilbao.
Atletico Bilbao dai suna son dawo da dan wasan Manchester United mai suna Heirera zuwa kungiyar, sai dai dan wasan yafison ya cigaba da zama a Old Trafford din.

An gayawa Manchester United su jira zuwa karshen kakar wasa ta bana domin daukan dan wasan baya na Napoli wato Koulibaly.

Manchester City zasu karawa Komapany kwantaragi.

Tsohon Coach din Arsenal wato Winger zai koma coach din kasar Qatar.

Bayern Munich tana daf da daukan dan wasan Chelsea wato Callum Hudson.

Chelsea suna neman dan wasan AC Milan wanda yake a matsayin aro a Savilla wato Andre Silva.

Barcelona sun tabbatar da cewa zasu sayar da Malcom da Danis Suarez.

Arsenal zasu mayar da tsohon dan wasansu mai suna d Edu director na kungiyar.