Gwamnatin tarayya ta bada umurnin sakin Dasuki da Sowore.

0

Gwamnatin Tarayya Ta bada umurnin sakin tsohon Mai Ba tsohon shugaban kasa shawara akan tsaro kanal ssambo dasuki Da kuma shugaban Yan zangazangar juyin-juya hali Sowore.

Ministan shari’a Abubakar Malami shine ya bayyana wannan umurni yana Mai cewa gwamnatin tayi hakan Ne Don Bi umurnin kotu Don mutunta dokar kasa.

Sannan yace Da fatan wadanda aka sakin zasubi sharuddanda aka gindaya masu Don mutuna dokokin kasa .

Tun a shekarar 2015 Ne aka Kama tsohon maiba tsohon shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro kanal sambo dasuki bisa zarginsa Da halatta kudaden haramun akan wasu kudaden makamai kuma tuni kotu ta bada belinsa amma gwamnatin taki sakinsa.

Shi kuma sowore shine shugaban Yan zangazangar nan ta “revolution now”wato juyin juya hali.

Shima kotun tabada belinsa amma gwamnatin taki sakinsa.

Gwamnatin Nigeria dai ansha kiranta gwamnatin Kama karya.

Dalilin Ki bin umurnin kotu misali.

Kotu tasaki malaminnan na gwagwarmayar Islam malam Ibrahim zakzaky amma gwamnatin taki sakinshi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.