Duk wanda ya kara zagina a yanar gizo, ko nawa zan kashe sai na sa an daureshi – Inji Ummi Zeezee

0

Duk wanda ya kara zagina a yanar gizo, ko nawa zan kashe sai na sa an daureshi – Inji Ummi Zeezee

Ta kacame tsakanin Ummi Zeezee da wasu a dandalinta na sada zumunta da muhawara na Instagram inda sukayi ta zage-zage, ta uwa ta uba irin wanda ba zasu maimaituba, a shekaran jiyane dai Ummin ta bayyana cewa hauka da rashin sanin ciwon kai yasa talaka har yanzu yake son Buhari duk da cewa bai cika alkawurran da yawa mutane ba.

dole.com ya wallafa labarin kuma labarin ya watsu kamar wutar daji, da alama wannan dalilinne yasa wasu, masoyan shugaban kasar suka je dandalin na Ummin sukata mayar mata da raddi abinda a karshe ya kare da zage-zage irin marasa dadinji.

Da abin ya isheta, Ummi ta bayya cewa daga yau duk wanda ya kara zaginta sai ta rama kuma zata sa ‘yan sanda su rika bibiyar duk wanda ya zageta, su shiga dandalinshi, suga inda yake zaune, kawai saidai yaga ‘yan sanda akofar gidansu, Ummi ta kara da cewa ko nawane zata biya dan taga an daure wanda ya zageta.

Related Of Current Post

Ku Danna Comment Domin Rubuta Ra'ayin Ku A Kan Wannan Post Din

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.