Direbobi sun rufe titin Kaduna zuwa Abuja bayan jami’an tsaro sun bindige wani direba

0 337

Direbobi sun rufe titin Kaduna zuwa Abuja bayan jami’an tsaro sun bindige wani direba

Kashe wani direba da jami’an tsaro su kayi a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya janyo direbobin sun fara zanga-zanga wacce ta janyo cinkoso a hanyar.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron sun harbe direban Peugeot J-5 din ne a kusa da Olam misalin karfe 7.30 na safe a hanyarsa ta zuwa Kaduna.

Sauran direbobin sun ga abinda ya faru hakan ya sa suka ajiye motocin su a kan titi suna zanga-zangar rashin amince wa da irin wannan kisar gillar.

Wani shaidan gani ido ya ce direbobin sun ki sauke motocinsu daga titin hakan ya janyo cinkoso a hanyar ta zuwa Abuja.

Ya kara da cewa a halin yanzu motocci duk sun tsaya cak duk da cewa ana karo wasu jami’an tsaro zuwa wurin.

Kwamishinan Harkokin Tsaron Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatarwa masu ababen hawa cewar za a warware matsalar ba da dadewa ba.

Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa: “Akwai cinkoso a kusa da kamfanin Olam.

Mun fara aiki kuma za a bude hanyar cikin kankanin lokaci.”