Daya daga cikin kyawawan jaruman Kannywood tace ta daina yin fim

1

Jarumar fina-finan Hausa, Halim Abdulkadir da aka fi sani da Intisar ta fito ta bayyanawa Duniya cewa ta fice daga masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood inda tace daga yau ita ba ‘yar fim bace.

A wani bidiyo da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta an ga Halima na fadin cewa “”Assalamu Alaikum jama’a suna na Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar, ina so nayi amfani da wannan damar na sanar da jama’a da masoyana cewa daga ranar irin ta yau 29 ga watan Agustan shekarar 2019, ni ba ‘yar fim bace ba, na fita daga masana’antar Kannywood.”

 

Halima ta kuma yi karin hasken cewa ba wai wani abune marar kyau ya faru ba da ya koreta daga masana’antar ba, kawai dai abinda ta yi tsammani ba shi ta tarar ba.

Ga abinda ta ci gaba da cewa”Kar mutane su dauka cewa wani abu ne marar kyau ya faru da ya sanya na fita, ba haka bane, tunda na shigo masana’antar nan ban taba samun wani tashin hankali da kowa ba, kawai dai wani daliline guda daya yasa na fita, abinda nayi tunanin zan gani a masana’antar ba shi na gani ba, abinda kuma nazo nema bashi na samu ba.

“Sannan ina rokon duk wanda na yiwa laifi ya yafe mini, nima kuma na yafewa kowa da kowa, na gode.”
Kalli bidiyon jawabin na Halima a kasa:

Leave A Reply

Your email address will not be published.

1 Comment
  1. Bello Hamisu says

    Your Comment Meyasa in dan zansaukar,da,kaset,baya sauri