Da Dumi Duminsa Uwa da danta sun kashe mijinta da duka

0 407

Uwa da danta sun kashe mijinta da duka

‘Yan sanda a jihar Naija sun kama wata mata, Hafsat Aliyu me shekaru 50 da danta Babangida Usman me shekaru 25 bisa laifin kashe mijinta,Aliyu Haruna.

Lamarin ya faru ranar 13 ga watan Afrilu a bayan makarantar Shango dake karamar hukumar Chachanga.

Sun amsa laifinsu inda Usman ya bayar da ba’asin cewa mahaifin nashi bashi da hakurine kuma da abu kadan ya hadasu da mahaifiyarshi sai ya kama cin zarafinta. Yace abinda ya faru kenan ranar kuma shi yana kokarin kare mahaifiyar tashine daga cin zarafin da mahaifinshi ya saba mata shine kawai ya fadi ya mutu.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da wannan lamari inda yace bayan dukan da wanda ake zargi sukawa Aliyu Haruna an garzaya dashi Asibiti amma kamin aje ya rasu. Ya kara da cewa za’a gurfanar dasu a gaban kotu bayan kammala bincike.

Ma’aikata 3 da ba zasu amfana da karin albashin dubu 30 ba