Bidiyon da ake yadawa cewa naje shakatawa a Amurka da matata ba gaskiya bane √ Kabiru Gombe

1 217

Bidiyon da ake yadawa cewa naje shakatawa a Amurka da matata ba gaskiya bane √ Kabiru Gombe

Da farko Sheikh Kabiru Gombe yace, “Wani ya yi rubutu a Facebook, kuma ya ce wani malami ne ya saka shi yin haka.
Malam Kabir Gombe ya ce “an yi rubutu an ce gashi bayan zabe Shugaba Bala Lau da sakataren sa gasu can sun fito yawon shakatawa bayan zabe ya kare, sun karbi kudin Buhari sun tafi yawan shakatawa”.

Sai Malam Kabiru ya tambayi mahalarta taron “shin na zo da matata kasar nan? sai duk suka amsa da a’a, ba ka zo da matar ka kasar Amurka ba.

Sai malam yace akwai wani bidiyo da aka yada wai nazo Amurka tare da iyalina da kuma shugaba muna shakatawa, sai yace, ya ce wannan bidiyo ba a kasar nan aka yi shi ba, ya ce akwai lokacin da muka je Umara tare da iyalina, sai wani abokina ya kawo min ziyara, shi abokin nawa mazaunin can kasar Saudiyya ne, sai daya koma gida sai ya fadawa iyalin sa, sai matar abokin sa tace ya kamata ka kai ni gun matar Sheikh mu gaisa sai ya kawo ta.

Bayan sun gaisa sai tace ma matar Sheikh ki roka mana malam mu je JIDDA ki ga ruwa mu dan fita shan iska haka, to bayan malam ya gama umra sai ya fita tare da abokin sa da matan su, su biyun, bayan sun isa JIDDA sai suka yi hayar jirgi suka shiga ruwa , malam yace sai matar sa tayi bidiyo.

Bayan ta yi bidiyo sai ta saka shi a Profile dinta, sai wasu mata suka dauke sai bidiyo ya fita.

Ya ce yanzu haka da fitar bidiyon ya kai shekara, amma magauta suka dauka suna yadawa akan mun ci kudin ‘yan siyasa sai muka fita tare da matan mu kasar Amurka yawon shakatawa.
Rariya.