Babu shirin cire tallafin man fetur nan kusa √ Ministar kudi

0 78

Babu shirin cire tallafin man fetur nan kusa>>Ministar kudi

Gwamnatin tarayya ta tabbatarwa da ‘yan kasa cewa bata da shirin cire tallafin man fetur nan kusa.

 

Ministar kudi, Zainab Ahmed ce ta tabbatar da hakan a wata ganawa da ta yi da ‘yan jaridu.

Zainab Ahmed ta fadi hakane a kasar Amurka wajan wani taron hadaka tsakanin Bankin Duniya da kungiyar bada lamuni ta Duniya, IMF.

Tace, babu shirin cire tallafin man fetur nan kusa.