
ALKUBUS MAI CARROT
Kayan Hadi
1)filawa
2) carrot
3)Mai
4)gishiri kadan
5)yeast
Yadda za'a hada idan zakiyi Kamar na tiya 1 saiki tankade filawarki ki kawo Mai kmr gwangwani 1 kisa sai Dan gishiri kadan sai yeast Shima kmr teaspoon 2 sai ruwa
Ana so kidan sawa yeat din ruwan gumi ki Fara motsa shi harya narke sannan ki juye a filawarki ki kawo Mai ki juye saiki kawo Dan gishirnki ki sa kadan sai ruwa shi ma bada yawa ba saiki kwaba ki buga sosai da kauri akeson kwabin inya bugu saiki rufe kisa arana
Bayan kmr awa 2 zai tashi in dai Baki cika yeast ba saiki Sami wurin da Zaki xuzzuba shi ki ki shashshafa musu Mai ki zuba dai dai yadda kk bukata dama kin gyara carrot dinki kin Yan yanka saiki diba ki xuzzuba akan kowanne gwangwani ko kwano inkina bukatar albasa ma Zaki iya yankata round haka ki jera a madambacin da kk hada kmr xakiyi dambu ki rufe bayan kmr 7 to 10 minutes zakiji kamshinsa na fita ko Kuma ki Sami tsinke Mai kyau ki tsira a tsakiya inya fito silif to yayi inya dibo Dan kullu Kuma saiki barshi ya kara