NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Kamar yanda Muka saba zamuyi bayani akan Ciwon mara Ga *mace mai ciki* Da kuma Ciwon mara ga *'yan mata* da kuma *Matan da basuda ciki* Da bayanin Ciwon mara bayan *mace ta haihu

Assalamu alaikum warahmatulah

*Toipc πŸ‘‰πŸ‘‰πŸ‘‰ kiyon lafia*
πŸ’ŠπŸ’ŠπŸ’‰πŸ’‰πŸ’ŠπŸ’‰

A yau topic din namu shine *Ciwon mara*

Kamar yanda Muka saba zamuyi bayani akan Ciwon mara Ga *mace mai ciki* Da kuma Ciwon mara ga *'yan mata* da kuma *Matan da basuda ciki* Da bayanin Ciwon mara bayan *mace ta haihu*

Idan mukace *Ciwon mara ga mace* toh abune Wanda Mafi yawa zai shafi *mahaifa* dalili kuwa saboda abinda mahaifa ta bakunta Wanda ba tasan dashi ba

Kafin mu shiga cikin topic zan danyi bayani kadan akan *uterus (wato mahaifa)* dakuma dalilin dakesa wannan *Ciwon mara*
Duk kowace Mace Allah ya halitta mata uterus saidai wata Allah ya kaddara ta haihu wata Kuma Allah bai kaddara da ta haihu ba Amma Kuma tana da mahaifa


Ita dai uterus (mahaifa) da kuka sani Kamar roba take. Yayin da roba tana sabuwa zakigan ta da kwari amma yayin data fara tsufa saita tsage ko ta fashe

Toh haka itama mahaifa take πŸ‘† yayin da duk ta fara haihuwa ko abortion toh karfinta zai fara ragewa
Sai dai ita uterus din mace kamar yanda scientist suka ce kamar kawchu take yayin da za aja kawchu yayi tsawo toh haka take yayin daukar ciki Zata Kara girma yayin da ciki yagirma kuma ita kulum tana bukatan Hutu yayin data fara aiki

Duk yayin da mace ta haihu tana bukatan Hutun haihuwa kimanin na shekara 3 saidai Wasu sun dauka cewa Hutu wato family planning kamar addini bai kawo Shiba suna kafa hujja da cewa kashe iyaline
Toh ko kadan ba haka ne
Ko Alkur'ani yayi zancan family planning inda yace mace mai Shayarwa zata shayar da danta Shekara 2 yace da wadda keso tacika shayar da danta

Idan muka dau wannan aya tana magana akan tsarin iyali yayin da mace ta shayar da danta Shekara biyu indan ta dau ciki Zata haihu bayan uterus ya huta kusan Shekara 3‬, Idan ba family planning mahaifa zata gaji, aikin da zata yi sai takasa daga karshe idan ta gaji sai ta tsage in kinyi sa'a a dinke bayan haka ba zaki dau ciki ba sai bayan shekaru 5 idan kuma kika dau ciki Kamin wannan shekaru toh Tabbas Zata Kara tsagewa kamar roba bayan haka bawata mafita saidai acire mahaifa duka Kuma keda haihu Bye Bye.
Don haka Ciwon mara ga mace abune Wanda zai shafi mahaifa ko ovaries ko trompe
Ita mahaifa girman ta bai wuce kamar a dunkule hannu yayin da ciki ya samu yana girma itama tana kara budewa kamar roba ko kawchu Dan haka yayin ciki ake kula da lafiyar mahaifa da abinda ke cikin ta

Sai dai ita wannan mahaifa tasha banban daga 'ya mace wata fatar ta tana da karfi toh haka wata kuma abu kadan zaisa fatar ta jimu toh haka itama mahaifa take
Mahaifar mace yana dauke da kalar halitta Wanda ke kewaye da ita da Wanda Kuma suke cikinta duk wannan halittu yayin da matsala ta shapi guda daga cikinsu Toh Tabbas zata shapi mahaifa
Idan ta shafi mahaifa Toh shine dalilin da kesa mace *Ciwon mara*
Kuma Ciwon mara ya danganta daga matsalar mahaifa wani zaiyi kamari wani Kuma idan Mara tayi ciwo kadan sai tabari Kuma in anjima ta koma ciwo wani Kuma kwata-kwata Ciwon mara zai dame shi ya hanashi sakat

Bakomi kesa haka illa bambanci mahaifa yayin da wani bako ya samu ko wani matsala
Don haka Ciwon mara abune Wanda ke shafar uterus ko Kingin (sauran) halittar dake kewaye da ita

Yayin Ciwon mara bai kamace ki zama Gida ba Dan bakisan kalar complication(matsalar) dake tattare dake ba
Ciwon mara mafi yawa 85% kamar yanda nayi bayani yana da alaka da mahaifa Saidai abinda ke sashi ita mahaifa tana da musclesπŸ’ͺ wato Wanda suke kewaye da ita yayin da matsala ta samu sai awannan musles πŸ’ͺ su tokare wuri guda basu aiki normal balle mahaifa ta zama cikin lafiya yayin da muscles sukayi haka πŸ‘† sai Mara ta kulle tafara ciwo

Sai mu shiga cikin topic din namu wato πŸ‘‰ *Ciwon mara*
Zamu fara da mace *Mai ciki* yayin ciki Nada *wata 3*

Na biyu Ciwon mara yayin ciki Nada wata *6 zuwa 9*

Sai Kuma Ciwon mara bayan *mace ta haihu*

Shine bayanin da zamuyi Idan Lokaci ya Ida

*Ciwon mara yayin ciki Nada wata 3*

Ciwon mara a wannan wattani ba abun wasa ne ba

Ko kunsan matsalar da ciwon mara yake iya kasancewa yayin wannan watanni (m'ana complication)❓❓

Kuma Miya kamaceki daki kula dashi yayin da Mara ta fara maki ciwo ❓
Kafin amsar wannan tambayoyi shidai Ciwon mara yayin ciki Nada wata 3 babbar matsala ce saboda idan Mace tayi wasa ciki yana iya zubewa ko ciki yayi wasa ko bayan haka zai iya sanadin rasa rayuwar yaro . Dan shine awanan watanni anaso mace tayi scanning (wato echographie) kuma tafara awon ciki.


Domin yin haka πŸ‘† zai taimaka wajan kiyon lafiyar ki da ta Yaron ki
Yayin wannan watanni ya kamata Kiyi test Wanda zai taimaka miki wajan Kare Lafiyar yaronki. Test din suneπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Test IVH (HIV)
Test hepatite( hapatitis)
Teste hg (haemoglobin)
ProtΓ©inurie (
Da sauran su.

3 complications ( matsala guda 3) wadda Ciwon mara yayin ciki Nada wata 3 yake iya kasancewa

Kuma duk kowane complication yana da illa sosai gareki

Dan haka sai ki kula domin lafiyar ki

Ga kalar complications (matsalolin) yayin Ciwon mara a wannan watanni πŸ‘‡πŸ‘‡
*Complication ( matsala) na 1⃣*
*Avortement (Miscarriage ) ma'ana bari*

Yayin da Mara ke ciwo zai iya sanadin bakin mahaifa ya bude Idan yabude toh abinda ke ciki shima zai iya zubewa( *bari*) idan ciki yazube a wannan watanni shi ake cema avortement (miscarriage)

Saidai miscarriage ( *bari*) yakasu gida 4
Shi bakin mahaifa bayada kokarin rike wannan ciwo idan Mara tafara ciwo toh bakin mahaifa sai yabude shine dalilin dakesa mace *bari*
Kuma ke baki iya gane yanda bakin mahaifar ki yake Dan shine ake so yayin Ciwon mara kije asibiti
Kamar yanda nace πŸ‘† kodai yayi silar zubewar ciki (wato bari)

*Shikuma zubar ciki Kala 4 ne*

1. menace d'avortement (ma'ana ciki yafara wasa ko yafara zuba)

Alamomin ciki yafara zuba
*ciwon mara*
*zubar jini*(wannan Kuma munyi bayanin sa
*bakin mahaifa yana rufe* (wannan Kuma baki iya ganewa sai likita ya tabbatar miki da haka

Wannan sune alamomin ciki yafara zuba

Toh minene yakamata yayin bayyanar wannan alamomi ❓❓❓❓
Yayin wannan alamomi babban maganin daza kiyi shine Hutu 100% πŸ‘‡
@ aikin gida ki Daina
@ duk wani abu mai nauyi ki daina dauka
@ sex(jima'i) shima ku Daina
@ kije Kiyi scanning
@ kifara awon ciki idan baki fara ba

Idan kika kiyaye wannan πŸ‘†πŸ‘† toh Mara da zubar jini zasu tsaya ki dawo normal bayan sati biyu Idan kinji Lafiya lau ne toh kina iya cigaba da aikin gida

Idan kuma kinada Hali likita zai samaki Magani Wanda zasu sa hormones dinki su rike cikin yanda bazai bare ba
Kamar πŸ‘‡

Uterogesten akwai 100mg ko 200mg (saidai shi 100mg kullum zaki sha da 1 shikuma 200mg zaki sha kullum guda da safe guda da maraice)

2.avortement incomplet (miscarriage incomplete)

Ma'ana ciki yazube amma akwai kingi (saura) cikin mahaifa (ma'ana ciki ya zube sai Yazama akwai Saura cikin mahaifa Wanda bai Ida fitowa ba)

Alamomin sa
#Ciwon mara
#zubar jini (munyi bayani akan sa)
# bakin mahaifa a bude
# abinda ke cikin ciki zai fito amma zaiyi Saura cikin mahaifa


Me ya kamaceki yayin wannan alamomi πŸ‘†πŸ‘†
Yayin wannan alamomi ya kamata ki πŸ‘‡
1.kije asibiti domin fitar da abinda yayi kingi (saura) cikin mahaifa (anacewa wankin mahaifa)
2. Bayan anyi aiki Sai kisha antibiotics akalla na sati 1 sabida gudun infection.
3. Sai Kiyi family planning nawata 3 domin mahaifa ta huta in Kam Bakiyi Hutu ba Toh shikesa da kin dauki ciki Sai ya zube har sai ya kaiki da daurin mahaifa (wato cerclage)
4. Bayan family planning na wata 3 zaki daina in kinaso ki fatan daukar wani ciki saboda bayan wata 3 dayin miscarriage mahaifa ta huta normal

‬Daga cikin Kalar miscarriage ga na 3 nana wato avortement 3 ,avortement complet (miscarriage complete)

Ma'ana ciki yazube duka babu sauran komi cikin mahaifa
Alamomin sa
1. zubar jini yanda duk wani abu Wanda ke cikin mahaifa zai fito duka
2. Ciwon mara
3. bakin mahaifa zai rufe dakansa bayan duk wani abu Wanda ke cikin mahaifa yafito


Miya Kamata gareki yayin da kikaji haka ❓πŸ‘†
Shi kuma wannan kalar miscarriage mata wanda suka yi haihuwa daga 5 zuwa 7 suke irin wannan kalar avortement(barin) sabida mahaifa ta saba Kuma bata Juriya ta yanda zata raga Saura

Kuma sabida su sunsan komi ta bangaran haihuwa mafi yawa basu zuwa asibiti wannan Kam baban kuskure ne ❌❌

Bayan haka yau da gobe Sai Allah ita kuma uterus guda ce.
*Yayin haka* tasha

# antibiotics na kimanin sati
#.family planning na wata 3
# bayan family planning na wata 3 Idan kinaso zaki iya Dainawa saboda a lokacin mahaifa ta huta.

Sai kachi na 4 Wanda shine na karshe daga cikin kalar miscarriage (bari) wato


*4.avortement inΓ©vitable*

Ma'ana bakin mahaifa a bude ciki duk yanda akayi ya zube amma Kuma yaki zubewa
Alamomin sa
#ciwon mara mai tsanani
# zubar jini
#bakin mahaifa a bude


Yayin haka miyadace gareki dakiyi ❓❓❓
Yayin haka Abu na farin
1. kije asibiti domin ko zaki Shekara a gida ina Mai tabbatar miki ba zai zube(bare) da kansa ba dole Sai anyi aiki an saka Magani Wanda zaisa bakin mahaifa yabude sosai Dan fitar da duk abinda ke cikin mahaifa
2.za abaki maganin dazai rage jin zafin ciwo
3.bayan Angama aiki zaki sha antibiotics (anan zaki sha na sati 2 saboda anyi aiki saman bakin mahaifa da kuma gudun infection ,
4.za a maki gwajin jini Dan a tabbatar da in babu cancer din mahaifa da na bakin mahaifa
5.za a maki allura wadda ake cema VAT( ita kuma allura ce wadda zata kashe duk wani dafi ko cuta wadda ke iya samun uterus ko col de l'uterus
6. Family planning saboda mahaifa ta huta Shikuma ana so kiyi na wata 3.


Shi ikuma wannan kalar miscarriage yafi kowane ciwo da wahala Ga mace Kuma matan da basu taba haihuwa ba ko masu haihuwa 1 ko 2 ko 3 sune mafi yawa Wanda suke irinsa

Saboda yana bukatar aiki
Bayan haka yakamata Kiyi scanning domin diba lafiar mahaifa
‬Wannnan Shine bayani akan complication na 1⃣ yayin Ciwon mara ga mace mai ciki yayin wata 3
Inda muka yi bayani sosai akan kaloli guda 4 na miscarriage wato (avortement )

Sai mu shiga *complication na 2* Wanda Ciwon mara ke iya kasancewa yayin ciki Nada wata 3
Kafin mu shiga cikin *complication na 2*
Zan danyi Karin bayani akan abinda muka fada a sama πŸ‘†πŸ‘†

Sanin kowane Ciwon mara ba yada dadi balle ga mace Mai ciki

Kisani yayin ciki duk wani Magani Wanda bana likita ba baj kamaceki ba ❌❌ maganin Hausa ba naki ne ba ❌❌

Zama da ciwon mara ki ki neman Magani bai dace gare kiba
Akawai matan da sunfi karfin suje asibiti sai ciwo yayi kamari(tsanani) Mace ta kusa mutuwa sannan akawo su asibiti

Wasu Kuma taurin Kai ne dasu

Irin wannan mata ana wayar masu da Kai gidan rediyo da asibiti da kalolin Magani kamar na Ciwon mara Wanda zasu siya susha Dan magance matsala Kar tayi tsanani
Yayin Ciwon mara akwai magani da yawa Wanda har inkin sha zakiji ciwo ya daina

Kalar maganin Ciwon mara shi ake cema Antispasmodique

Kuma akwai Wanda zaki sha da ruwa Kuma akwai na matsi duk kalar halin ki(ma'ana yananyin kudin mutum ) zaki samu Magani daidai da kudinki
*Antispasmodique* shine Magani Wanda ke warkar da ciwon mara
Gasu Kamar haka πŸ‘‡πŸ‘‡

Nospa 80mg ko 40mg
Spasfon
Gynosfan
Spasmo -apotel
Bytul
Nospa forte
Phloroglucinol 80mg
Meteospasmyl
Solispasm
Spasmodex
Spasmocalm
Spassirex 80mg
Genotropine
Wadannan sunne kalolin maganin Ciwon mara
Yayin Ciwon mara kina iya neman daya Daga ciki

Kalar halinki(kudinki) kalar maganin ki

Complication na 2⃣
*GEU ( grossesse extra utΓ©rine )*

Ma'ana ciki a *gefen mahaifa* ( wato ciki Ya zama baya cikin mahaifa Sai dai yana wajen mahaifa)

A ka'ida ciki yana girma cikin mahaifa ne amman yayin wannan matsala Toh ciki zai tsaya cikin ovaries ko trompe, Kuma yace anan zai girma abinda Kuma bai yiyuwa ❌❌

Yayin da Mace Zata dauke ciki Toh wannan kwai na halitta da farin zai tsaya cikin ovaries sawon kwna 3 da Sannu sai yazo cikin mahaifa sai yaci gaba da girma

Amma yayin da bai iso cikin mahaifa ba shine ake kira da wannan complication GEU

Alamomi wannan complication GEU

#Ciwon mara
# zubar jini ( saidai Jinin zai zuba can cikin mahaifa ba a ganinshi a farjin mace)
# idan akayi scanning babu komi cikin mahaifa sai dai acan wajan su ovaires Za aga cewa ciki anan yake
# Ciwo a gefe guda dama ko hagum
# Mace Za tai ta zufa
# yawan faduwar gaba
# shock


Wannan sune alamomin dake tabbatar da haka saidai yayin wannan alamomi sai anyi scanning domin a tabbatar da haka πŸ‘†

Bayan scanning Sai a kwantar ma mace da hankali domin komi nufin Allah ne
Minene mafita yayin wannan *complication GEU*❓❓❓


Mafita guda shine

Laparatomie ( wato CS)
Babu wani πŸ’Š ko πŸ’‰ Wanda zasu sa yadawo cikin mahaifa sedai Kawai cs Shikuma CS za ayi Shi domin a cire wannan ciki
Bayan an Cire cikin daga cikin ovaires toh Shikenan babu ciki❌

Bayan cs
Sai family planning na Chekara 3

*Complication 3⃣ Grossesse molaire*

Shikuma wannan complication kadan daga cikin Mata Ake samu masu wannan complication kimanin 9%

Shikuma yayin da ciki Nada sati 5 zai bayyana da ciwon mara mai Tsanani, zubar jini
Scanning ke tabbatar da wannan matsalar

Yayin haka shima ciki bai tsayawa sai anyi aiki domin a fitar dashi

Bayan haka sai family planning na shekara 1 Kuma duk bayan sati 4 anaso mace tayi test har tsawan shekara 1 Idan test ya bada positive toh dalili dake nuna mace tanada cancer

Sai a duba aga cancer din na mahaifa ne koko cancer din na ovaries ne

Bayan haka sai ashiga maganin cancerShikuma cancer zai iya zama na mahaifa ko na ovaires ko trompe

Sai dai shi irin wanan cancer babu ❌❌ wasa a ciki wajan neman Magani in abu na sauki za a cigaba da magani in ana Magani Abu babu dama Toh dalili ne Wanda zaisa Sai ancire wurin da cancer ya shafa

*Lafia uwar jiki babu Mai fushi da ita*
Wannan chine bayani akan Ciwon mara yayin ciki Nada wata 3
Inda muka yi bayani akan complication guda 3 Wanda Ciwon mara yake iya sakawa

Bayan haka sai muka yi bayani akan kowane complication inda muka yi bayani sosai akan kaloli guda 4 na miscarriage inda Muka bada alamomi da Kuma yanda ya kamata ki kula da kuma kalar treatment


*Allah sa ku anfana har Kuyi ma Wasu gargadi*


‪Sai muchiga kachi na 2

*Ciwon mara yayin ciki Nada wata 6 zuwa 9*


A wannan watani ya kamata ace

Kinyi awon ciki na 2 yayin ciki Nada wata 6 ✔
Kiyi scanning ✔

Cikin wata na 8 zuwa wata 8 da Rabi
Shima Kiyi awon ciki na 3
Kiyi scanning


Mace wadda tasan 'Yancinta ita ke awon ciki sau 3 yayin ciki Kuma tayi scanning sau 3

Mace Kuma masu hikima da basira da sanin ya kamata su suke awon ciki sau 4⃣ yayin ciki da kuma scanning 4
Badan komi ba Dan kiyon lafiyansu da Yaron su


Allah sa matan sirri kuna cikin wannan mata πŸ’‍♀

*Ciwon mara yayin ciki Nada wata 6 zuwa 9*


Sai kubiyoni domin jin ko Wane dalilai kesa Ciwon mara yayin a wannan watani

Kuma Wane complications ake iya samu ❓

Wane alamomi ke bayana cewa Ga kalar complication ❓

Mine ne mafita da yanda ya kamaceki yayin da wannan complications suka bayyana ❓
Amsar wannan tambayoyi da bayani akan *Ciwon mara yayin wata 6 zuwa 9*

Sai wani sati In shaa Allah in muna cikin masu rai πŸ‘
Ramly πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ–Š
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts