NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

DUKKANIN LITTATTAFAN DA ALLAH YA AIKO ANNABAWANSA DASU SUNYI BUSHARA TARE DA BAYANI AKAN MANZON ALLAH (S.A.W) DA SAHABBANSA.


DUKKANIN LITTATTAFAN DA ALLAH YA AIKO ANNABAWANSA DASU SUNYI BUSHARA TARE DA BAYANI AKAN MANZON ALLAH (S.A.W) DA SAHABBANSA.
.
Admin maijidda Bello

Allah madaukakin sarki ya aiko Annabawansa mabanbanta, da littattafai mabanbanta, amma kuma kowanne Annabi saida yayi bushara tare dayin bayani akan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da sahabbansa, tare da yin nuni akan cewa shari'ar da zai zo da ita duk ta shafe tasu kamar yadda Allah Subhanahu Wata'ala yayi bayani a wurare daban-daban cikin Al-Kur'ani mai girma.
.
Muhammad Manzon Allah (S.A.W) da wadanda ke tare dashi masu tsanani ne akan kafirai, amma masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganin su suna masu ruku'u, da sujjada, sa’ad da suke neman falala daga Allah da yardarsa, alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujjada, wannan shine siffarsu a cikin Attaura, kuma siffarsu a cikin injila ita ce kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sannan yayi tsaho yayi girma, ya kuma farantawa manoma, ta haka ne yake fushi da kafirai, Allah yayi wa'adi ga wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, daga cikinsu, da gafara da sakamako mai girma.
(Suratul Fathu, aya ta 29).
.
Sa’ad da kuma Isah dan Maryam, yace: "Ya Bani Isra’ila, ni Manzon Allah ne zuwa gareku, mai gaskatad da abinda ke gaba gareni na Attaurah, kuma mai bayar da bishara da wani Manzo dake zuwa a bayana, sunansa Ahmad (mashayabo)." To, sa’ad da ya nuna masu hujjoji, sai suka ce, "Wannan sihiri ne, bayyananne."
(Suratul Suff, aya ta 6).
.
A wani ingantaccen hadisi kuma, Manzon Allah (S.A.W) yace "Nine addu'ar Annabi Ibrahim (A.S), nine busharar Annabi Isa (A.S) nine mafarkin mahaifiyata".
.
Kai! Wannan Annabi da girma yake, madalla da watan Rabi'yul Auwal, madalla da 12 ga wannan wata, madalla da ranar zuwan fiyayyen halittu duniya.
.
Allah ka kara mana kaunar Manzonka, ka bamu albarkacinsa duniya da lahira.
Ahlan bi shahril mauludi, Da'iman sai Manzon Allah (S.A.W).
.
Abba Ahmad Gwammaja.
20/11/2018

From admin maijidda Bello
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts