NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

AMFANIN TUMATIRI A JIKIN DAN ADAM!!!

a by admin maijidda bello Tumatir yana da Iron, in kana fama da cutar fatarar jini, to juice din Tumatir, cinsa danye zai taimaka ba kadan ba, za a iya maganin ko sauqaqa , haka zai taimaka wajen magance toshewar numfashi, sinadarin cikin tumbi da yake taimakawa wajen niqe abinci in ya yi yawa, sauran cututtuka na qirji ma Tumatir kan taimaka matuqa, yana ma da amfani ga masu cutar sukari, sabo da Carbohydrates din dake ciki bai da wani yawa, akan yi aiki da shi wajen rage qiba, in ba a yi aiki da shi yadda ya kamata ba kishiyar hakan za ta bayyana, amma Tumatir ya qunshi abubuwa da dama kuma masu amfani, mu tara a shiri na gaba mu gani.

TUMATIRI A JIKIN DAN ADAM!!!

Tumatir dai mahadi ne sananne ga mutane masu dama a mabambantan abinci, kodai a dafa shi, ko a soya, ko ma a ci danye, yana da kaloli daban-daban, amma wanda aka fi sani shi ne ja, sai dai akwai ruwan lemo, rawaya har ma da ruwan malmo, gwargwadon qasashen da suke amfani da shi, a taqaice dai, wasu fa'idoji ne ake samu a cikin Tumatir?

Ya za mu yi aiki da shi don samun fa'idojin da suke cikinsa?

Ko yakan yi maganin wasu cututtuka?

Shi kuma me da me ya qunsa?

Ko cinsa da yawa zai iya wahalarwa?

Wadannan da wasunsu muke so mu tattauna a ciki in sha Allahu ta'ala.

Tumatir daya ne daga cikin jinsin yalo, amma ana daukarsa a matsayin ganyayyaki sabo da Antacid, ana qiyasta cewa Tumatir yakai kala 600 a duniya, Tumatir yana da amfani a jiki gwargwadon yadda mutum zai ji ya kuma kiyaye, yakan taimaka wajen kawar da qwayoyin cutar da suke cutar da jikin dan adam, yakan dawo da nashadin qoda yadda zai yi aiki kamar yadda ya dace sabo da samun Vitamin A, C mai dama a cikinsa, yakan yi aiki a matsayin sinadarin wanke ciki da hanji, yakan kawar da wahalar da ciki yake fama da ita wajen markade abinci, sananne ne cewa Tumatir ya qunshi Iron, wanda yake fama da fatarar jini zai iya shan juice din Tumatir ko ya ci danyensa.

Akan yi aiki da Tumatir don magance gurbataccen ruwan sinadarin dake jiki, haka wahalar yin numfashi da wani lokaci yakan yi wahala ga dan adam, yakan yi amfani ga masu ciwon sukari, sabo da ba shi da Carbohydrates mai yawa a cikinsa, haka ciwon gabobi, Tumatir kan magance shi ta wajen zuba masa mai a dan ba shi tsoro a wuta sai a shafa a inda yake cutarwan, kasancewar Tumatir yana dauke da kashi 95% na ruwa yana iya daidaita qibar mutum, ga shi bai da Calories mai dama.

Tumatir yakan samar da Vitamin C mai kyau, Provitamin A ko Carotene, Vitamin A wanda yake Antioxidant ya taimaka wa garkuwar jiki, wani binciken ya nuna cewa yakan yi maganin wasu nau'o'i na Cancer ciki har da na mabubbugar maniyi, da na huhu, sabo da yana dauke da sinadarin Lycopene wanda shi ne yake sanyawa launin Tumatirin ya zama ja, Tumatir yana dauke kuma da Minerals wadan da ake dan shan wahalar samu, irin su Potassium da yake inganta qoda, da Phosphor, Calcium da Magnesium.

Fatar Tumatir da 'ya'yan cikinsa sun qunshi sinadarin da yake taimaka wa hanji, Antacid din kuma zai kyautata aikin niqe abinci yadda zai agaza wajen zuqo mafificin Nutrients, Tumatir in aka lura ya qunshi Vitamins B, Vitamin C, Iron, Potassium, Calcium da Magnesium, ga shi yana da mahimmanci wajen zama rigakafin wasu cututtuka, bincike ya nuna cewa, mutanen da suke da Lycopene mai dama a jikinsu hatsarin daskarewar qwaqwalwa ba ta da yawa, wata da ake kira Daniella ta ce gaskiya bincike ya tabbatar da cewa Tumatir bai hana Cancer din qwaqwalwa amma zai iya magance kumburinta.

Duk da cewa launin Tumatir wani daban ne da wani, sai dai suna da sinadarin Lycopene gaba dayansu, wanda yake maganin tattarar fuska, Tumatir yakan fitar da Antioxidant wato Lycopene don kare fata, ko hana tattarar fatar, duk da cewa ba mai wani babban tasiri ba ne amma dai yakan yi, ta ce cin Tumatir din da yawa ba ya nufin zai magance matsalolin gaba daya, sai dai ta yi nunin cewa Tumatir din yana dauke da sinadarin Tyramine da Serotonin da dan dama wanda yakan taimaka wajen canza wa mutun yanayi, har ya ji duniyar ta yi masa daidai.

Tumatir ya qunshi Vitamins ne kawai da Minerals, Fibres, Protein da Carbohydrates, amma bai da Sodium, da Saturated fats da Cholesterol, yana da Vitamin A mai kyau, Thiamine, Niacin, Vitamin B6, Folic acid, Magnesium, Phosphor da Copper, kuma yakan samar da Nutrients mai kyau, Vitamin A, C, K, Potassium da Manganese, daga cikin fa'idojin Tumatir akwai kawar da Germs, wadan da suke haifar da cututtukan jikin dan adam, Tumatir kan motsa nashadin qoda, yakan yi aiki a matsayin mai wanke hanji, kamar yadda yake kau da wahalar niqe abinci, ko fitar da shi bayan ya gama amfani.

Tumatir yana da Iron, in kana fama da cutar fatarar jini, to juice din Tumatir, cinsa danye zai taimaka ba kadan ba, za a iya maganin ko sauqaqa , haka zai taimaka wajen magance toshewar numfashi, sinadarin cikin tumbi da yake taimakawa wajen niqe abinci in ya yi yawa, sauran cututtuka na qirji ma Tumatir kan taimaka matuqa, yana ma da amfani ga masu cutar sukari, sabo da Carbohydrates din dake ciki bai da wani yawa, akan yi aiki da shi wajen rage qiba, in ba a yi aiki da shi yadda ya kamata ba kishiyar hakan za ta bayyana, amma Tumatir ya qunshi abubuwa da dama kuma masu amfani, mu tara a shiri na gaba mu gani.

Zamu cigaba in sha Allah
2 Comments5 shares
99
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts