NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^ . LITTAFI: BAYANI AKAN DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNA

WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA'EED GAMAWA.
.
___FITOWA TA 46 NA KARSHE___
.
WANENE MAI DA'AWAH !!!
.
DAGA: Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe [Secretary General, JIBWIS, Nigeria]
.
Da yawa mutane na zaton cewa kira zuwa ga Musulunci da nusar da musulmi kan turbar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), aiki ne da ya rataya kan manyan maluma da wadanda ke da ruwa da tsaki acikin harkar addini.
.
Aikin fadada musulunci, isar da shi gyarawa mutane zama nauyi ne da ya rataya kan kowane musulmi da musulma. Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Ku isar da sako daga gare ni, ko da aya daya ce kawai kuka sani.” hakanan sau da yawa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) idan ya kammala zance sai yace: “Wanda yazo ya sanarwa wanda basu samu damar zuwa ba.” Ashe duk wanda yasan aya daya nauyin kira zuwa ga addinin ALLAH ya hau kansa, in ji Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam). Don haka iyayenmu dattawa da abokai na samari, ya zama tilas akan mu duka damu isar da sakon musulunci gwargodon hali. Kuma kowa ya tambayi kansa, wacce gudumawa ya bayar wajen habaka Musulunci. Hakika kowa za'a tambaye shi kan damar da aka bashi, ya yayi amfani da ita ?
.
Muyi hattara cikin nasihohi da amsa tambayoyin mu ga 'Yan uwa kada muyi kari ko ragi ko kago karya ko nuna son zuciya. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Wanda yayi min karya da gangan ya tanadi matsuguninsa a wuta ranar al-kiyamah.” ALLAH Yasa mu dace, Amin.
.
TSAYAWA KAN KOYI DA SUNNAH WAJEN YADA DA'AWAH !!!
.
DAGA: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo [Shugaban Majalisar Malamai JIBWIS, Nigeria. 11/01/2914]
.
'Yan uwa Musulmai, babban Malamin Musulunci Al-Hafiz Ibn Rajab wanda ya rasu a shekarar hijira ta 795 yayi wata magana da ya kamata a rubuta ta da ruwan zinare, yace acikin littafinsa mai suna [Alhakamul-Jaduratu bi iza'ah, shafi na 12.]
.
“Wajibi ne akan dukkan wanda Umurnin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya isa zuwa gare shi, ya kuma san shi, ya bayyana shi ga al'ummah, yayi musu nasiha, ya umurce su da bin umurninsa koda kuwa hakan ya sabawa ra'ayin wani babba acikin al'ummah, saboda Umurnin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) shi yafi cancantar girmama shi, kuma ayi koyi dashi akan ra'ayin dukkan wani wanda ake girmamawa, wannan shi yasa sahabbai da wadanda suka biyo bayansu suka yi wa dukkan wanda ya sabawa sahihiyar hanyar sunnah raddi.....”
.
'Yan uwa Musulmai, dukkan abunda mutum yasan cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi umurni da yinsa, to wajibi ne ya bayyanar da shi ga Al'ummah, sannan da za'a samu wani mai son zuciya yayi kokarin hana shi yin hakan to bazai saurara masa ba. Haka nan haramun ne akan kowane musulmi ya bi ijtihadin wani malami komai girmansa matukar ijtihadinsa ya sabawa nassin aya ko hadisi ko ijma'i ko qiyasi, kamar yadda sheikh Usman Bin Fodio ya fadi.
.
ALLAH Ya tabbatar damu kan Yada Da'awah ta gaskiya, Amin. Wannan shine KARSHEN LITTAFIN !!!
.
BAYANIN MAI GABATARWA: Alhamdulillah ina matukar farin ciki da godiya ga ALLAH da bayani iko da damar rubuto wannan littafin a Social media sannu a hankali har zuwa FITOWA 46. Ina kuma addu'ar fatan alkhairi ga jinjina ga Mawallafin wannan Littafin wato SHEIKH ALIYU SA'EED GAMAWA Hakika Malamin yayi matukar kokari wajen wayar mana da kai game da DA'AWAH da abubuwan da suka kebantu da ita, ga duk mai son sanin Hakikannin DA'AWAH to hakika idan ya karanta wannan littafin zai samu ingantaccen bayani daga koyarwar ALQUR'ANI da SUNNAH. Kuma littafin yana nan a kasuwa. ALLAH Ya sakawa Malam da alkhairi tare da dukkan Malaman mu da suka sadaukar da rayuwar su ta hanyar bawa Addinin Musulunci gudumawa, wadanda suka rigamu gidan gaskiya ALLAH Yayi musu Rahma (Ameen)
.
Ina kuma fatan alkhairi da godiya da addu'a ga Dan'uwa M.UMAR BIN KHAMIS wanda shine ya bada shawarar a rubuta wannan littafin a Social Media saboda amfaninta ga al'ummah, sannan kuma ya turo min da littafin har gida, ALLAH Ya saka masa da alkhairi tare damu baki daya. (Ameen)
.
Ina yiwa dukkan Admins da Members na ZAUREN MUSLIM UMMAH tare da dukkan masu bibiyar Rubutukan mu a Sahar social media fatan alkhairi, da addu'ar ALLAH yasa mu amfana da abunda muke karantawa, Ya kuma yi mana muwafaka da dukkan ladan, abunda muka rubuta bisa kuskure ALLAH Ya gafarta mana, ALLAH Ya kara daukaka Musulunci da Musulmai. (Ameen)
.
'Yar-uwarku a Musulunci: Faridah Bintu Salis [Bintus-sunnah] from admin maijidda bello daga sirrin yamace
.
Zaku iya liking page dinmu:
.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts