NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MATSAYIN MATA DA GADON SU A MUSULUNCI daga malam aminu ibrahim daurawa

MATSAYIN MATA DA GADON SU A MUSULUNCI

MUSULUNCI YAZO YA SAMI MATA A CIKIN KUNCI, DA TAKURAWA DA TSANANI, DA RASHIN KIMA DA DARAJAR YADDA AKE MU'AMALA DA ITA A DUNIYA,
1 MUSULUNCI YA HANA KASHE MACE.
2 MUSULUNCI YA HANA BINNE MACE DA RANTA.
3 MUSULUNCI YA HANA TOZARTA MACE.
4 MUSULUNCI YA HANA DUKAN MACE.
5 MUSULUNCI YA HANA YIWA MACE AURAN DOLE.
6 MUSULUNCI YA HANA KWACEWA MACE SADAKI.
7 MUSULUNCI YA HANA GADAR MACE A MATSAYIN KAYAN GADO .
8 MUSULUNCI YA HANA YIWA MACE AURAN DOLE.
9 MUSULUNCI YA HANA YIWA MACE CIN FUSKA.
10 MUSULUNCI YA WAJABTA A CIYAR DA MACE, AKAN MAHAIFINTA, IDAN TANA DIYA, IDAN TANA MATA AKAN MIJINTA, IDAN TANA UWA AKAN YA'YA'NTA.
11 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA TAYI ILMI.
12 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA TAYI SANA'A
13 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA IDAN BATASON MIJI TA RABU DA SHI TA HANYAR KUL'I.
14 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA TAYI IDDA A DAKIN MIJINTA BAYAN YA SAKE TA.
15 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA TA RIKE YA'YA'NTA BAYAN SUN RABU DA MIJINTA.
16 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA TA MALLAKI, DUKIYA, TA HANYAR SANA'A KO AIKI KO GADO.
17 MUSULUNCI YA BAWA MACE GADO, 1/8, KO 1/6 KO 1/4 KO 1/3 KO 1/2 KO 2/3 KO KUMA A BATA DUKA.
18 MUSULUNCI YA YADDA MATA SU SHIGA CIKIN AIKIN IBADA, SUJE MASALLACI, SUJE HAJJI, SUYI AZUMI, SUYI ZAKKA , SUJE IDI. SUJE KASUWA DA WAJAN SANA'A WACCE TA DACE DA SU.
19 MUSULUNCI YA BAWA MACE DAMA DA YANCIN BAYYANA RAAYINTA,
20 MUSULUNCI YA TOSHE DUK WATA KAFA TA TSANANTAWA MACE, KO TAKURA MATA, KU YUNWATATA, KA KARUWANTAR DA ITA, KO AMFANI DA ITA DON BIYAN WATA BUKATA, TA SIYASA KO TA ADDINI, KO KASUWANCI, DA MAKAMANTANSU.
MAFI YAWAN MASU KIRA AKAN YANCIN MATA BASU SAN YADDA MUSULUNCI YA TSARA YADDA , ZAA ZAUNA DA MATA BA, KO KUMA BASA AIKATA YADDA MUSULUNCI YA FADA,
ALLAH YA RABAMU DA SON ZUCIYA
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts