NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MAGANIN YAWAN AMAI GA MATA MASU JUNA 2

MAGANIN YAWAN AMAI GA MASU JUNA BIYU

TAMBAYA TA 2572
*******************
Assalamu alaikum malam mai zauren fiqhu da fatan katashi lafiya da iyalan gidanka ameen.

Malam ina tambaya akan mace mai sabon ciki menene ya kamata abata don rage wahalar ciki da laulayi, kamar amayi, tofar nyawu da sauransu.

Nagode Allah yakara dokaka darajarka da gidanka ya kuma jikan iyaye was salam.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ka samu danyar citta (raw ginger) ka matseta ka samu ruwanta kamar cokali guda. Sai ka hada da ruwan dafaffiyar Habbatus Sauda, shima cokali guda. Ka sanya cokali guda na zuma ko Ma'u Khal (sai abinda ta za'ba).

Ka bata tasha safe da yamma, cokali daya ko biyu. In shaAllah zata dena yawaita aman, kuma zata samu karfin jiki koda bata cin abinci sosai ba zata rame ba. Saboda ita zumar tana bama gangar jiki dukkan sinadaran da take bukata.

Bayan haka asamu ganyen Na'a-Na'a adafa ataceshi sannan a zuba garin Kirfi tare da lemon tsami (idan bata da Ulcer) sannan azuba zuma a bata ta rika sha safe da rana da yamma.

Allah yasa adace ameen.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (30/09/2018 20/01/1440).
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts