NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MAGANIN TALAUCI A MUSULUNCI

MAGANIN TALAUCI A MUSULUNCI !!!
Za a iya kau da Talauci ne bisa mahangar Musulunci ta wadannan Hanyoyi:
1. Zaburar da Mutane kan a tashi a nemi abin Kai tare da samar musu aikin yi, Annabi yace:
“Dayanku ya je bayan Duwatsu ya tara Kirarra ya goyo shi a Bayansa, ya kasa ya sayar ya fi masa Alkairi da ya ringa rokon Mutane.
Annabawan Allah na da Sana’a Haka Magabatanmu na Kwarai, Ko ka taba karanta Litattafin Khallal?
2. Inganta Hanyar Zakka tare da rabata kan tsarin da Musulunci ya shinfida.
3. Mawadata su ringa kyautatawa na kusa da su, tare da kokarin Rayar da su ba bautattar da su ba, musamman Danginsu na Jini.
4. Amfani da Baitul Mali(Public Account) don inganta rayuwar Jama’a ba Azurta kai ba, Misali kan haka Inganta tsarin Waqafi dss.
5. Dorawa wadanda su ka aikata wassu Laifuka cire wani abu na Dukiyarsu don a mikata zuwa ga Fakirai da miskinai.
6. Kwadaitar da Al’umma Sadakar Zabin Kai, hakan a fili yake cikin dimbin Hadisan da suka kwadaitar da taimakawa masu Kananan Karfi.
7. Addu’a, Don Manzon Allah yana neman tsari daga Talauci da Lalaci.
8. Dakile Bara da Tumasanci da dabi’ar Allah ba ku mu samu.
9. Bin Yayi yana durkusar da halin Kirkira, wanda shine matakin habaka kowace Al’umma, Manzon Allah yace:
“Ka da Dayanku ya zamanto; Imma’a(Bi Yarima ka sha Kida) Tirmizy.
10. Adalci, domin shine ginshikin ci gaba da dorewar kowane Tsari.
Allah ka rabamu da Talauci ka kuma wadata mu daga falalarka, Ameen.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts