NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

KASUWANCI MAI RIBAR GASKE !!! .

KASUWANCI MAI RIBAR GASKE !!!
.
Hakika ALLAH (SWT) ya fifita mutum akan sauran halittu kuma ya kebe mutum da ni'imta shi da yin magana, ya sanya na'urarsa itace «HARSHE» Ni'ima ce wadda za'a iya amfani da ita wajen aikata alkhairi ko sharri. Duk wanda yayi amfani da ita wajen alkhairi lallai ya rabauta a duniya da masaukai madaukaka acikin aljannah. Duk kuma wanda yayi amfani da ita akasin haka (wato ta sharri) to lallai halaka ta riske shi duniya da lahira. Mafificin lokacin da mutum zai rabauta dashi bayan karanta Alkur'ani maigirma sai ZIKIRI (ambaton ALLAH).
.
ALLAH (SWT) yayi bayani a wurare da dama acikin littafinsa game da ZIKIRI (ambaton ALLAH) daga ciki yake cewa:
.
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُوا لِي وَلَا تَكْفُرُونِ
.
“Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini.” [Baqara: 152]
.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا
.
“Ya ku wadanda kuka yi imani ku ambaci ALLAH ambato mai yawa.” [Ahzab: 41]
.
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
.
“Da masu ambaton ALLAH da yawa maza, da masu ambatonsa Mata, ALLAH ya tanadar musu gafara da lada mai girma.” [Ahzab: 35]
.
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
.
“Kuma ka ambaci Ubangijinka acikin Zuciyar ka, kana mai kankantar da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba, da safe da mare ce, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu.” [A’araf: 205]
.
→ Ya tabbata acikin hadisi masu yawa, daga cikin fadin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Shin ba na baku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu awajen sarkin da yake mallakarku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alkhairi daga gare ku daga ciyar da zinari da azurfa, kuma mafi alkhairi gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku ringa dukan wuyoyinsu suna daukan wuyoyinku ? Suka ce ka bamu labari, sai yace: Ambaton ALLAH Madaukaki.” [Tirmizi]
.
→Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda baya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce.” [Bukhari]
.
→ Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “ ALLAH madaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawa na da ni, kuma ina tare dashi idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni acikin ransa zan ambace shi acikin raina, idan ya ambace ni acikin jama'a zan ambace shi acikin jama'ar da tafi su alkhairi, idan ya kasance ni taki daya, zan kusance shi kamu guda, idan ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaba guda, idan yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa.” [Bukhari]
.
→ Daga Abdullahi Ibn Busr (RA) yace: Ya Manzon ALLAH! Shar'o'in Musulunci sunyi yawa agare ni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riko dashi, sai yace: “Kar harshenka ya gushe face yana danye daga ambaton ALLAH.” [ Tirmizi, Ibn Majah]
.
Ana ninninka sakamakon ayyuka na Kwarai saboda gwargodon yawan tunanin zuciya da ambaton ALLAH da kuma mai da hankali akan haka, bawa idan ya tuna da ALLAH a lokacin da yake cikin yalwa, ALLAH zai tuna shi alokacin da yake cikin tsanani, musamman a halin mutuwa da magaginta.
.
Acikin zuciya akwai gurbin talauci babu abunda ke toshe shi sai ambaton ALLAH (SWT), karancin ambaton ALLAH alamar Munafurci ne, yawaita shi kuma Alamar karfin imani ne da kuma gaskiyar soyayya ga ALLAH, domin duk mai son wani abu zai yawaita ambaton shi.
.
Harshe na samun kariya daga wasanni, da cin naman mutane da Annamimanci, karya da sauransu na abubuwan 'ki da kuma haramun.
.
ZIKIRI Yana koran shaidan, yana takura shi, yana wulakanta shi kuma yana kaskantar dashi, kuma ALLAH (SWT) yana yarda da mai AmbatonSa.
.
ZIKIRI Yana gadar da soyayyar ALLAH da kuma kusanci zuwa gare shi da kuma samun kwarjini daga gare Shi.
.
ZIKIRI Yana gusar da bakin ciki da damuwa kuma ya sanya farin ciki da gadar da rayuwa mai kyau da karfi da kuma tsarki.
.
ZIKIRI Waraka ne ga Zuciya kuma magani ne gare ta, kuma dalili ne na samun karfi, da jindadi wanda babu kamar sa, kuma gafala daga barin ambaton ALLAH ciwo ne ga Zuciya.
.
ZIKIRI dalili ne na samun tsira daga azabar ALLAH (SWT) da kuma samun nutsuwa lullubewar rahama da kuma samun neman gafara daga mala'iku.
.
ZIKIRI shine mafi sauki daga cikin ibadoji, kuma shine mafi girma da falala kuma dashi ne ake samun shiga gidan Aljannah.
.
ZIKIRI Na gadar da kwarjini da jindadi da kuma annuri (haske) ga fuska, shi haske ne anan duniya da kabari da ranar alqiyama.
.
ZIKIRI Na haifar da samuwar yabo daga ALLAH (SWT) da kuma mala'iku ga mai yinsa, ALLAH (SWT) Yana alfahari da masu ambaton Sa.
.
ZIKIRI Na saukaka wahala, kuma yana saukaka tsanani, yana kuma saukaka kunci, yana jawo arziki kuma yana karfafa ruhi da jiki.
.
Mafifita daga masu bauta sune wadanda suka fi ambaton ALLAH (SWT) da yawa, kuma wadanda suka fi falala daga masu yawaita Azumi sune wadanda suke ambaton ALLAH (SWT) a lokacin Azuminsu.
.
→Babban Malamin nan Ibn Taimiyyah (Rahimahullah) Yace: “Zikiri ga Zuciya kamar ruwa ne ga kifi, to yaya rayuwar kifi zai kasance idan har ya rabu da ruwa?”
.
ALLAH shine mafi sani
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts