NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HUKUNCE-HUKUNCEN TAKABA A SHARI'AH [1]

HUKUNCE-HUKUNCEN TAKABA A SHARI'AH [1]
.
DAGA: Malam Abuna'ila Saminu.
.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
.
✿ Ma'anar Takaba: Takaba a yaren larabci itace ﺍﻹﺣﺪﺍﺩ (Kauracewa ado)
.
→Ma'anar ta a Shari'ah: lokacin da matar da mijinta ya mutu ya bar take dauka, tana mai nisantar yin dukkan abunda zai sata Jan hankalin namiji ko aji ana sha'awarta ko son kallonta, na daga ado ko duk abunda ya dauki ma'anar hakan, har zuwa tsawon lokacin da shari'a ta kayyade mata.
.
✿ RABE-RABEN TAKABA: Takaba ta rabu kashi biyu: (a)Ta Shari'ah (b)Ta Jahiliyya (maguzanci)
.
❖ TAKABAR SHARI'AH: Itace wacce ta dace da umurnin ALLAH da ManzonSa. sannan ta kasu kashi biyu:
.
1● Takabar matar da mijinta ya rasu.
.
2● Takabar matar da wani nata ya rasu ba mijinta ba.
.
❖ TAKABAR JAHILIYYA: itace wacce ba a dora ta akan umurnin ALLAH da ManzonSa ba, ita ma iri biyu ce kamar haka:
.
1● Wacce ake yinta kafin zuwan Musulunci tun lokacin iyaye da kakanni.
.
2● Wacce zamani yake kawo ta dangane da cigaba da kuma banbancin al'adu.
.
✿ HKIMAR YIN TAKABA: Musulunci ya wajabta Takaba ne saboda hikimomi masu yawa kadan daga ciki:
.
→ Girmama Aure da nuna matsayinsa da daukakarsa.
.
→ Girmama hakkin miji da kiyaye dangantakar da akayi dashi.
.
→ Sanyaya ran makusantan miji da nuna damuwa da abunda ya same su.
.
→Toshe kafar mace ta ringa tsammanin aure da wani, ko kuma maza su ringa kawo mata caffa. Domin cike idda da duk abubuwan da suka shafe ta.
.
→ Nuna alhinin kubucewar ni'imar aure wacce ta taro alkhairan duniya da lahira.
.
→Ba wa rai damar numfasawa da nuna abunda ya same shi na bakin ciki ta hanyar da bata sabawa shari'ah ba.
.
Mu hadu a Rubutu na [2] inshaa ALLAH.

15 Comments60 shares
3030

Maijidda Bello

Maijidda Bello

W
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts