NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

BUSHEWAR GABA (DRY VAGINAL) . Wannan a hausance na nufin karancin ni'ima ga mace kamar yadda matan sukafi fada. Amma


πŸ’πŸ’πŸ’ SIRRIN YA MACE GROUP πŸ’πŸ’πŸ’

Admin maijidda Bello
From admin jeddatulkhari tijjani adam

BUSHEWAR GABA (DRY VAGINAL)
.
Wannan a hausance na nufin karancin ni'ima ga mace kamar yadda matan sukafi fada. Amma mu a kimiyyance mukance karancin, damshi ko lubrication a farjin mace inda hakan ke jawo jin zafi Yayin saduwa, rashin jin dadin jima'i, rashin sha'awar ko jin tsoron a kusanceta saboda Wahalar da takeji da kuma radadi cikin farjin da sauransu.
Hakan na faruwane sakamakon karancin sinadarin Estrogen ajika Wanda shike Samar da damshi cikin al'aurar wato (ni'ima) dama sauran mahimman abubuwa ajika da kara jin dadin gamsuwa yayin saduwa, domin estrogen shine mai habbaka shawa'awar jima'i awasu inyai kasa shike sa basu da karfin sha'awa sosai.
.
ME KE JAWO HAKAN ?
Kamar yadda akaji karincin sinadarin estrogen ke jawo bushewar farji, sai kuma sauran ababe kamar:-
.
1)- Magungunan da akesha masu karfi musamman a mutane masu ciwon sanakarar nono (Breast Cancer), duk maganin dazai yaki ciwon cancer ajika ka iya jawo haka tawani bangaren.
.
2)- Tsiron cikin mahaifa wato (fibroid).
.
3)- Matsalar dakan shafi cikin mahaifa wadda ba Kari ba.
.
4)- Rashin haihuwa.
.
5)- Tiyatar kwayayen haihuwa a mace (ovaries) watakil ko adalilin cyst.
.
6) - Sai stress, depression da kuma Radiation. Wato damuwa da kuma yanayin aiki kamar masu aiki a radiology department, masu dealing da image ko masu aiki aguraren hada bomb da alburusai.
.
7)- Motsa jiki fiye da kima (Intense exercises).
.
8)- Sai kuma amfani da sabulai, omo, mayuka, turare da kwaroron roba ta hanyar cusasu akai akai ba precautions.
.
ABUBUWAN DA HAKAN KAN JAWO
A)- Yana jawo yeast infection tare da rauni acan cikin farji.
.
B)- Jin zafi Yayin saduwa, musamman idan namijin bai iya foreplay ba gashi kuma me naci.
.
C)- Rashin gamsuwa, tunda jima'i arai yake Amma jikine keyi yayin da ake cikin damuwa ita bazata ji dadi ba komi zakai.
.
D)- kaikayin gaba da sauransu.
.
ME KE FARUWA A ASIBITI
Mukan yi abunda ake cewa Colposcopy (wato examination of the vagina) a duba ko akwai rauni a farjin, kuraje, dad'ewa ko kuma Yanayin canjin launin kala.
.
MAGANCEWA
1): Bada magani ya danganta da abunda binkice ya nuna shi ya jawo hakan, Amma muna bada magani mai kunshe da sinadarin estrogen din sannan kuma mukan bada magunguna dangin antibiotics, anti fungal, anti inflammatory dadai sauransu bayan mutum anyi masa gwaje gwaje da aune aune bada ka ba, kuma sai a manyan asibitoci ba sha katafi ba.
.
2): Sannan kuma akwai mayukan Lotion na musamman wato vaginal lubricants da ake bayarwa suna taimakawa wajen samun jin dadin jima'i da samun gamsuwa ta hanyar shafasu a wajen ba masu illa bane dazasu bada matsala.
.
3): Duk mai wannan matsalar ta daure taje ta sami kwararrun jami'an lafiya a fannin wato (Gynecologist) don su dubata su bata magani bawai matsalace daza a bada magani online ba a'a nan saide shawara magani ko sai anyi kafa da kafa tukun.

Admin maijidda Bello ✍️
&
Jeddatulkhari tijjani adam

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts