NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

maganin kone kitse ne (fat) na gargajiya wanda yake kunshe da abububuwa 3

AJu MBAISE*: maganin kone kitse ne (fat) na gargajiya wanda yake kunshe da abububuwa 3: ganye, saiwa da kuma sassaqe.
Sunan maganin ya samo asaline daga mutanen garin AJu MBAISe (wani babban gari ne dake jihar imo) daya daga cikin jihohin kasar nan tamu wato Nigeria.

Matan garin suna amfani da wannnan magani domin rage tumbin da suka samu sanadiyar ciki, suna amfani dashi ne bayan sun haihu.
Ana dafa maganin nan tare da :1)masoro 2) gyadar kamshi ta hausa (nutmeg),da 3)kimba.

*Wa ya kamata yayi amfani da aju mbaise*?

*Mai jego*: yana taimakawa wajen wanko dukkan wani ragowar datti na ciki, yana maganin ciwon ciki na mai jego sannnan yai mata maganin tumbi, cikinki ya dawa normal.

*Matar da tumbi yayi mata yawa*

*Matar da take son rage kiba*

*Amfanin Aju mbaise*:
1)Yana taimakawa wajen fidda dukkan wani mataccen jini dake cikin mai jego, sannnan ya taimaka cikinta ya dawo kamar yanda yake ada.
2) yana dawo da al'adar da ta dauke,yana daidaita al'ada, yana taimakawa mata wadanta al 'adarsu ke zuwa kadan kadan sannan yana maganin ciwo yayin al'ada.
3)Matar da tayi Bari:yana wanko mata ciki ya fidda dukkan wani abu da yayi rogowa a cikinta yayin da tayi wannnan bari, zata samu saukin daukar ciki a duk lokacin data shirya daukan wani cikin.
4) masu matsalar rashin haihuwa: yana taimaka musu wajen wanko musu dattin mahaifa da ikon Allah.

Yana maganin warin baki wanda yake fitowa daga cikin ciki.

Yana taimakawa mata masu matsalar ovulation .

*Yanda ake sarrafashi* zaa wankeshi tas da ruwa mai tsafta a yanda yake (kada a warware shi)
Sai a saka cikin tukunya madaidaiciya, sai a xuba ruwa kimanin liter 4 sai ki kawo wannan kayan hadin ki zuba ciki ki rufe ki barshi ya dahu sosai a hankali amma kada ki cika masa wuta don kada ruwan ya kone , ki barshi yayi kaman 15-20minutes
Zaki ga kalarsa ta chanja yayi duhu kaman ruwan lipton (shayi) sai a sauke a tache a bari ya huce.
A ringa shansa da dumi kamar tea.
Cup 1 da safe kafin kaci komai 1 da rana 1 da daddare bayan awa 2 ko 3 da cin abinchi (ya zama shine na karshe) .

NB: za kiyi amfani da kulli daya sau 3 kafin ya salamche.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts