NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HADIN SINASIR

♛♛♛ SANWA ADON MACE♛♛♛

Assalamu alaiku

MAtan sirri Saboda yawan bukatun ku na
mu koya muku yadda ake yin wainar
shinka da kuma sinasir yasa a yau
muka samar muku cikakken bayani
kan yadda zakuyi.

Abubuwan da zaki bukata

1.Fararar shinkafa
2.Shinkafa ta dafawa
3.Yeast
4.Sugar
5.Baking Powder

Da farko dai za muyi misali ne da
shinkafa rabin kwano.
Ki sami farar shinkafa rabin kwano ki
wanketa ki jika, idan
ta jiku, sai ki sami shinkafa wadda ake
dafawa a ciki, 'yar
Hausa ko kuma 'yar
gwamnati gwangwani biyu, ki
dafata, amma kar ki dafeta lugub,
garau-garau zaki yi
dahuwar, bayan kin dafa sai ki juyeta
a cikin farar
shinkafar da kika jika, ki markadota.

Yanzu sai ki zuba
yeast da sugar ki dama yadda
zasu narke, sai ki ajiye kullin a waje
mai dumi dan ya tashi,
idan ya tashi sai ki dauko tandar ki in
waina zakiyi idan
kuma sinasir zakiyi sai ki dauko kaskon
suyar sinasir
din, dama tuni kin tanadi ma suyarki
sai ki zuba a kaskon kafin ki zuba
kullin, yadda dai ake yin kowa ce irin
waina.
Shikenan ana iyaci da miya etc

#ADMIN_MAMANFAISAL (maijidda bello)


SINASIR DA MIYAR TAUSHE

MIYAR TAUSHE
Ingredients
Zaki samu tumatur,albasa,attaruhu,saiki markadasu.Ki yanka alayyahu,lawashi,albasa.Saiki dafa kayan miyan harsai ruwan kayan miya ya Kame,ki dafa nama da maggi da albasa ki ajiye a gefe.Saiki samu tukunyarki ki zuba kayan miyan,da mai,ki dan saka manja cokali daya,saiki soya kamar minti goma,inya soyu saiki zuba gyadar miya adadin yadda kikeso(kiyi amfani da gyada mai bargo tafi gardi a girki),kiyita jujjuyawa kamar na minti goma,saiki zuba maggi,curry,gishiri adadin taste dinki,saiki zuba ruwa kadan,kin wanke allayyahunki da lawashi saiki zuba a ciki ya dahu kamar na minti Bihar,saiki juye namanki a ciki shima ki juya,ki juyasu duka su hade,saiki barshi ya kara minti biyar saiki kashe.Shikenan

SINASIR
Ingredients
Farar shinkafa
Yeast
Baking powder
Albasa
Sugar
Salt
Man gyada
YADDA AKEYI
Zaki jika shinkafarki iya adadin yadda kikeso,zaki jiya na 8hrs.Idan ta jiku sai ki tace ruwan ki yanka albasa kadan,anfison farar albasa,Saiki kai nika,idan aka niko saiki zuba yeast dinki a ciki,ki tabbata yeast dinki mai kyau ne,kuma dadan yawa yadda zai tashi,saiki juya sosai,saiki ajiyeshi karkashin rana na 30minutes,idan babu rana saiki ajiye wuri mai dumi,idan ya tashi saiki kuma juyawa ki saka baking powder a ciki,itama ki tabbata mai kyau,ki sami ta gwangwani tafi kyau,saiki juya ki zuba sugar kadan kada yaji zakwai,ki zuba gishiri kadan.Saiki samu nonstick frying fan dinki ko kuma tandar sinasir saiki dinga zuba mai kadan kina zuba kullin kamar yadda zakiyi wainar fulawa,amma ana rufewa da murfi saboda saman yayi,saboda ita baa juyawa


MU KOMA KITCHEN!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
★★★SINASIR★★★★★★★★
Yan Uwa na wannan gida Assalamu alaikum Warrahmatullah.
Bayan lokacin Mai tsawo gamu mun dawo.Filin nan ne da mukan gabatar
nida abokiyar aikina watau kauthar
Usman gashi dai naxo idan kun shirya nima haka.
Shida dai sinasir kaman masa yake anaci da miyar ganye shima.
ABUN BUKATA
☆Shinkar tuwo
★Gishiri
★Mangyada
★Baking powder
★Yeast

YAN DA XA A HADA.
Xaki tuka tuwon shinkafa kaman gwanngani madara daya.

Sai ki nemi shinkafarki ta tuwo dai dai yawar iyalinki,ki jikata ko ta kwana ko awa daya ma xatayi,ki wanke ta ki kai nika,kafin ki tafi sai ki dauko tuwon shinkafar ki murjeshi sosai cikin jikakar shinkafa da xaki kai nika sai ki kaita a markada su tare,ki xuna yeast dinki 1/2 teaspoon.,Sai ki rufe ta xuwa awa daya sai ki bude kisa gishiri kadan da dan sugar sai ki rufe ki shirya toyawa amma kwabin sinasir xai fi ruwa kadan ki dauko non stick frying pan,kisa a wuta ki shafa mashi mangyada,kafin ki fara xakisa baking powder itama pinc,sai ki duba in ya yi xafi sai ki fara idan kika xuba kaman xa ai pan cake xai baje a haka sai ki rufe idan yayi a juye har a kare.
Anacinshi da miyar kabewa da alayahu ko dage dage.Allah yasa mu dace amin.
A madadin abokiyar aikina Kauthar Usman ni jagoran shirn taku har kullum(Husnah Asma u A Muhammad nake cewa mun gode sai wani satin inshaalla.kafi nan ina nan shigowa da gyaran jiki wajen karfe 5 na yamma inshaAllah. — feeling wonderful.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts