NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

BAYANI AKAN CUTAR MASTITIS -Wannan cuta ce dake haifar da zafi kan nonuwa, taurin nonuwa da kuma chanzawar kalar fatar nonon zuwa ja.----------------------

BAYANI AKAN CUTAR MASTITIS
------------------------------------------
Wannan wata cuta ce da ke faruwa a nonuwan mata, mafi akasari wannan cutar tana samuwa ne ga mata masu shayarwa (Lactation Mastitis) a cikin sati 6 zuwa 12 bayan haihuwa.

Amma wasu lokuttan takan kama mata wadanda basu shayarwa.

Wannan cuta ce dake haifar da zafi kan nonuwa, taurin nonuwa da kuma chanzawar kalar fatar nonon zuwa ja.

ABUBUWAN DAKE KAWO WANNAN CUTA
-------------------------------------------
Ababe 2 ke kawo wannan cuta:
1. Toshewar hanyoyin gudanar madarar ruwan nono.
Wannan na faruwa ne a sakamakon rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki

2. Shigar kwayar cutar Bacteria:
ALAMOMIN CUTAR MASTITIS
--------------------------------------
Alamomin sun hada da:

* Breast tenderness (Taurin nonon idan an taba sa)

* Generally feeling ill (malaise) (Zazzabi mai nauyi)

* Breast swelling (Kumbirewar Nonon)

* Pain (Jin zafi yayin da yaro ke shan nono)

* Skin redness (Chanxa kalar fatar nonon zuwa Ja)

YAUSHE NE YAKAMATA KIGA LIKITA
----——----------—--------------------
A duk lkcn da kika ga mafiyanci daga cikin wadannan alamomi wadanda suka wuce awa 48, to ki tuntubi likata zai dora ki akan shawarwari da magani.

MATAN DAKE KAN HATSARIN KAMUWA DA WANNAN CUTA
----------------------**--*---------------------------
* mata masu shayarwa sati 6 zuwa 12 bayan haihuwa

* Macen da ke da rauni akan kan nonon.

* Matan da basa chanzawa yaro nono idan ya shanye dayan

* Matan dake amfani da biresiya mai matsewa yayin da suke shayarwa

MAGANIN MASTITIS
---------------------------
Oral Antibiotics ne ake amfani da shi wajen magance wannan cutar

HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR
-------------------------------------------
1. Cin abinci maigina jiki
2. Tabbatar da karewar ruwan nono 1 kafin a chanxawa wa yaro 1
3. Daina amfani da matsaystsiyar biresiya yayin shayarwa
4. Ki tabbatar da kin shafe ruwan nono a kan bakin nonon bayan yaro ya gama sha
5. Ki tabbatar da sai ruwan nonon ya kare kafin ki baiwa
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts