NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YADDA ZAKI HADA BAKAR HUMRA MAI KAMSHI TAKI KONA SIYARWA
BAKAR HUMRA
‘yan’uwa mata in a yi muku tuni da ku rike turare da kyau, dan turare maganadisu ne na jan hankali, amfanin da turare a jikinki, sutturarki, gidanki yana sa megida ya kara samun nutsuwar zama da ke, kuma ko yaushe zai dinga son kasancewa da ke…
@ BAKAR HUMRA @
& mahala
& hawi
& farce
& turaren marakana
& turaren sondol na ruwa dan awo
& turaren amarya
& madarar turaren abaraidadi
& madarar turaren suzan
& turaren me sanyin ruwa kalar da kike so mara mai ko
_> yadda zaki yi ki dake mahala dinki, bayan kin soya sama-sama sai ki dake ta ta yi laushi, shi ma hawi ki dake ki tankade ,ki jika farcenki a ruwan omo ko clean, idan yayi kamar awa biyu da jikawa, sai ki dora farce da kika jika da ruwan clean ya yi ta dahuwa, har sai yayi kamar awa biyu ko uku ruwan na tafasa da farcen a ciki, sannan ki sauke ya huce, sai ki sami reza ko brush din goge baki ki dinga kankare farcen da rezar ko brush din, daya bayan daya, wannan nama-naman da ya taso na jikin farcen sai ya fita gaba daya, idan kin gama kankarewa sai ki shanya farcen ya huce, sannan ki zuba farcen a kasko kiyi ta juyawa a kan wuta har sai farcen ya kone yayi baki, sannan ki dake yayi laushi sosai
yadda zaki hada shi ne ki zuba ruwan turarenki na marakana kwaiba daya ta awon mankuli, sannan ki zuba turaren sandol na ruwa gwangwanin madarar ruwa guda daya, turaren amarya ma gwangani daya, turare me sanyi ruwa mara maiko kalar da kike so gwangwani daya, ki sa madarar turaren aborai dadi cikin kwaibar fiya-fiya ta madarar suya ma cikin kwalbar fiya-fiya ki sa garin mahala cokali biyu na abinci garin hawi cokali biyu garin farce ma cokali biyu ki juya sosai, bayan kin gama hadawa sai ki rufe humrar ki barta ta tsumu a gun mai zafi ko ki dora kaya a kanta inda ba zata sha iska ba har zuwa sati daya ko biyu ko sama da haka, idan ta tsumu sosai ta yi kamshi
zaki iya yin humra da ruwan turaren amarya wato ya fi yawa turaren marakana kuwa sai ki sa gwangwani daya yadda dai kike so, wannan dakakken su farcen zaki ga in kin zuba kwalba suna yin kasa, amma zai saka humrar ta dinga kara tsumuwa tana kara kamshi
@ FARAR HUMRA @
turaren alajin na ruwa ko na marakana ko na matan arewa
+ jan ambur
+ farin ambur
+ misik
+ madarar turaren kwamando
+ madarar turaren suzan
+ madarar turaren sarkin turare
+ madarar turaren sandol
+madarar turaren ismiyaki
zaki yi ki daka farin ambar dinki wanda ake sayarwa a kasuwa guda uku, sannan ki daka jan dan kanti guda uku, sai ki zuba a kan ruwan turaren alajin ko marajana ko matan arewa roba daya, ki sami misik dinki guda hudu ki zuba a kofin silver ko a tukunyar silver ki dora a kan garwashi zai narke, idan ya narke sai ki yi sauri ki juye a cikin ruwan turaren da kika zuba garin abubuwan, sannan ki daka misik din ki sa cokali uku sannan ki zuba madarorin turaranki ko wanne cikin kwalbar fiya-fiya ki jua sosai ki rufe ya tsumu, wannan garin misik dinda ambar din shi zai dinga kara tsuma humra ta dinga kara kamshi za ki iya rufewa kwana bakwai ko zuwa sati biyu ta tsumu
TURAREN WUTA NA DAKI
amma shi wannan yadda ake hada shi dabban ba da kyau kuma da irin kamshinsa duk da itacen irin daya ne , abin bukata sune:
% farce
% sukari
% lemon tsami
% jawul fari
% misik
% garin sandol
& madarar turaren jamila
+ madarar turaren wanis
+ madarar turaren sabon yayi
& madarar turaren binta sudan
& madarar turaren kamfani
+ madarar turaren naludu
& madarar turaren dan duwala
& madarar turaren kafin kafi
& madarar turaren sandol
& madarar turaren abarai dadi
+ turaren ruwa mai maiko
yadda zaki yi ki sami itace al’ud dinki daya, ko biyu sai ki jika shi da madarar turaren jamila da madarar turaren wanis, da madarar turaren sabon yayi, sannan ki sa turarenki mai maiko na ruwa irin wanda ake aunawa a dogwayen kwalabe sai ki jika da wadannan turaruka ki rufe ki bar shi ya jiku har yayi kwana, bakwai bayan sati daya sai ki bude itacen alud din da kika jika da turare, idan kuma kilo daya ne sai ki sa gwangwani daya, idan sukarin gwangwani biyu ne sai ki zuba ruwa cikin karamin kofi ki matsa lemon tsami hudu a kai, ruwan sukari, idan kuma gwangwani daya ne sai ki zuba ruwa rabin karamin kofi ki matsa lemon tsami biyu a kai sannan ki saka garin jawul cokali daya da ruwan lemon tsami da sukarin ki sa misik kwaya uku a ciki, sannan ki debi garin farcen da kika barza ki zuba kadan a kai amma shi ma farcen zaki gyara shi kamar irin gyaran da aka ce za’a yi masa a hadin humra, sai dai shi bayan an soye barje shi ba daka shi lukwi ake yi ba idan kin zuba sai ki bar shi yayi ta dahuwa har sai ruwan sukarin ya fara ja,sannan ki zuba itacen al’aud din naki a kai kiyi ta juyawa idan ya dahu sosai sai ki sauke ki juye a faranti ki baza sannan ki zuba garin sandol dinki a kai da garin dakakken misik da garin dakakken jawul
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts