NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

SUNAYEN MAGANUNNUWA DA AMFANINSU GA LAFIYAR DAN-ADAM MACE👩🏻 KO NAMIJI👨🏻SUNAYEN MAGANUNNUWA DA AMFANINSU GA LAFIYAR DAN-ADAM MACE👩🏻 KO NAMIJI👨🏻

1- HABBATUSSAUDAH (BLACK SEED)
Hayaki da yayan habbatussaudah a jiki, ko a tsakar gida yana korar shetanu, kuma yana kau da bakincikin da yake da nasaba da shetanu👺, me fama da Ciwon daji ko gyambon da ya ki warkewa ya hada ruwan khal tuffa🍏 da Zuma waje daya, sai ya dinga wanke gyambon yana barbada garin habbatussaudah a kan gyambon, ko daji in ya fashe.

HULBAH (FENUGREEK):
Hulbah tana maganin gyambon ciki (Ulcer) musamman in ana zuba ta cikin madara ana sha da garin habbatussaudah, ana amfani da hulbah don gyara ruwan Nono don shayar da jariri👶🏻 musamman man ta, shan man hulbah ko garin ta cikin ruwan zafi🍵☕ yana taso da sha'awa, hulbah tana maganin amosanin kah👴🏻 musamman in an wanke kan da sabulun salo, sai a hada garin hulbah da man zaytun sai a shafe kan gabadaya bayan an aske gashin kan, in mace CE kuma sai ta dinga kitso da shi. Sit birth da yayan hulbah yana kara santsin farji ga mata👩🏻

HABBATURRASHAD
Za a ga garin ta kaman an daka gyada, in ana shanta da Zuma tana kara ruwan sperm ga maza da mata, tana yaki da cutukan da ke cikin jini, tana gyara uwar hanji.

FULASKO (SANAMAKI)
Yana wanke ciki da Mara yadda ya kamata, musamman in ana shansa cikin shayi ba madara, kuma yana narkar da tsakuwar da ke cikin Qoda (Appendix), yana maganin basur dankanoma in ana sha a cikin kunu ko koko.

GIRFAT
Tana maganin tari, yana daidaita hawanjini, Yana kara karfin mazaqutar da namiji, sannan yana bubbude kofofin numfashi misali huhu (lungs).

NA'A-NA'A (MINT)🍃
Yana maganin tari, yana karfafa zuciya wajen haddace karatu😇, yana maganin tari na mura, ko busashshen tari, yana maganin zazzabin typhoid, yana maganin kaikayin makogwaro da na hanci, yana kuma maganin Sanyi me kama ga6o6i in ana shafa mansa a jiki.

MAN GELO
Yana maganin aljanu in ana shafawa ga jiki, amma ana hada shi da man zaytun kafin a shafa saboda bakin sa. Ana shan man gelo chokali biyu a ruwan zapi, sai kuma a hadiyi tafarnuwa sala daya, a sha ruwan khal chokali biyu bayan cin abinci🍝 wannan zai magance cutar basur ko wanne iri ne.

HIDAL
Ana shan garin hidal da Zuma domin maganin dukkan matsalar da take cikin ciki, ana hada hidal da Zuma da garin yansun domin maganin farfadiya😬😇 ko maganin Ciwon hanta ko Ciwon zuciya❣ ko kuma Ciwon Mara ko matsala ta SHETANUN aljanu👺👹

GANYEN ZAYTUN🍃
Ana hada ganyen ko garin zaytun da tsohuwar tsamiya daidai misali, sai a jika ya kwana sai a sha yana maganin Ciwon ciki ko wanne iri, garin zaytun yana maganin kowacce irin cuta musamman sihiri ko jinnu, ko cutar da ba a gane kanta ba.

KHISTIL HINDI
Za a ganshi garin sa fari ne me yaji, yana yawan sa attishawa😤 ana dafa shi ana sha da Zuma yana maganin jiri ko Ciwon kai, yana maganin SHETANUN Aljanu👺👹 Yana gyara ma'aikatar numfashi (lungs) huhu.

QURNUFUL/KANUNFARI (CLOVES)

Yana maganin Ciwon hakori in ana daka garin ana kwabawa da mansa ana sawa a inda hakorin ke ciwo😬 ana sit birth da shi don kau da kaikayin gaba ko matsalolin farji, yana maganin zazzabi in ana dafa shi da habbatussaudah ana sha kaman shayi☕ da zuma

ALBABUNAJ
Yana maganin fitar aljanu👺 in ana dafawa ana shansa, kuma yana maganin matsalolin mata in ana dafa shi ana sha da Zuma, akwai ganyensa🍃 kwai kuma furensa🌼 kowanne yana da amfani ga LAFIYAR ma'aikatar sha'awa. Yawanci dafawa ke ana sha kaman tea da Zuma.

SAZABU
Ana dafa garin sazabu ana wanka da shi don warfare sihiri ko fitar da aljani, ana shansa da Zuma ta asalin marar hadi don maganin Ciwon Mara ko ciki lokacin jinin al'ada🌡 ana hada shi da albabunaj ana dafawa ana sha don samun Haihuwa a gun Allah☝🏻

MA'UL-WARDHI (ROSE WATER)
Ana hada shi da ruwan zam-zam da ciyawar Za'afran🍁 da kuma lubban zakar (Qaro), domin magance matsalar ta6un hankali😇 ko sumbatu, ana sha ana shafawa, kuma wannan hadin yana maganin rikirkicewar Al'amura musamman kasuwanci.

JIR-JIR (KARASS)
Yawan cin karass yana magance matsalar mahaifa ga mata👩🏻 amfani da mansa, da kuma man danya a hade, yana maganin matsalar Rashin haihuwa👩🏻

ZAYTUL-LAUZ (MAN DANYA)
Yana maganin Ciwon Mara, yana taimakawa wajen wanke mahaifa, yana maganin samun Haihuwa ga mata👩🏻

TAFARNUWA (THAUM)
Tana maganin miyagu, mayu, basur, Sanyi me kama ga6o6i, infection, ta hanyar dafa yayan ta ana sha da kaninfari da Zuma kaman tea☕ tana maganin aljanu👹👺

BUZUR FIJIL
Yana maganin yoyon mahaifa wato yawan 6arin juna biyu. Yana wanke marar mata.

HILTI (HALTITI)
Yana shaqe aljanu😬👹, akwai duwatsunsa, akwai kuma garin sa, ana shakar garin ne ta hanci (snipping). Duwatsun kuma ana tsotsa ne kaman alawa (mint) ana hadiyewa, kuma yana karya sihiri, yana maganin Ciwon kai.

MUR
Yana maganin Ciwon ciki me Tsanani😭

AL-MAQDUNAS
Yana cire aljanu da kau da cututtuka da suka shafa aljanu ko sihiri.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts