NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

SIFFOFIN MACE SALIHA* Wallafar : *Shaik Adamu Muhammad Dokoro* *Fitowa ta 001**SIFFOFIN MACE SALIHA*

Wallafar : *Shaik Adamu Muhammad Dokoro*

*Fitowa ta 001*

Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki,tsira da aminci su tabbata ga manzon Allah da sahabbansa da matansa,da sauran wad'anda suka bishi da kyakkyawan har zuwa ranan saka mako.

Bayan haka, kafin mu shiga bayyana siffofin da ya kamata mace ta cikasu kafin ta bada wata gudumawa, ya kamata muyi wata tambaya kamar yaka . *wacece mace* ? : Mace dai wata halittace wacce Allah ya halitta mai raunin gaske kuma wata kuma wata halittace mai wuyan sha'ani .Shiyasa Manzon Allah ( ) Yace" *KAJI DA'DI DA ITA A KARKACE*" ma'ana shine mace fa ba zata mike kan hanya ba sai ba sai ta wahalar ,wanda kuma yakeson zama da ita dole yayi hakuri domin ba zata bi hanya mikakkiya ba. Shiyasa Manzon Allah ( ) Yace " *IN KAJE DOMIN KA MIKAR DA ITA ZAKA KARYATA, KAYARTA KUMA SHINE SAKETA*" Haka kuma yazo a Alqur'ani mai girma Allah Yace " *MACE MUN KAGETA DAGA ADO KUMA BATA IYA BAYANI IDAN TA HA'DA WAJE SAI KUKA*" Wannan yana nuna maka zatayi wuyan sha'ani don haka mai zama da ita sai ya tanadi hakuri mai yawa da juriya kamar yadda yakamata domin zai yi fama mai yawa ,Allah Yabamu sa'a amin thumma amin.

1, *Mace kafun musulunci* : Ita mace kafun zuwan musulunci tasha wahala awajen mazaje da addine daban-daban kamar yadda tarihi ya hikayo mana wasu addinai suna ganin yakamata a hana mace wanzuwa a wannan duniya gaba d'aya domin bata da amfani a duniya sai musifa.Wassu addinan kuma suna ganin tana da amfani ga mai gidanta amma inya mutu bata da amfani wannan yasa suke konata tare da maigidan nata da ranta don ya rigata mutuwa.

Wasu addinan kuma suna ganin bai kamata mace ta mallaki koda sisin koboba domin bata da 'yanci na mallaka don haka da ita da kud'inta da komai nata mallakan mai gidantane itama kanta kayansace bata da 'yanci .Wasu addinan kuma suna ganin mace bala'ice suna mata kirari da cewa bala'i musifa wanda akama ado a tsakar gida.Jahiliyar larabawa tanaga yakamata akashe 'ya mace da ranta a kuma binneta da ranta ,kai wannan azaba tayi yawa da kuma kafirci amma musulunci ya fitar da ita daga wannan wulakanci izuwa mutunci amma kuma sai ga mace tana cima kanta mutunci tana wulakanta kanta wai hakan shine mutunci.

2, *MACE DA UBANGIDANTA* :Farko dai dole tayima Allah d'a a ta zai da sallah tayi azumi tayi zakka tayi aikin hajji kamar yadda akeso ,ta kyaukyata akidarta ga Allah mad'aukakin sarki tasan bawani abun bautatawa da gaskiya sai Allah Shi kad'ai. To in tai wannan tasami babban fandisho wanda zata dora komai na ayyukanta kuma su amfaneta.

*Allah Yasa Muna daga cikin wad'annan mata* (Amin)

A sauraremu a fitowa na 2 in shaa Allah.

✍🏻 'Yar uwarku a musulunci:
*Ummu Abdillah Gombe*


Admin maijidda Bello *
Repost

*September 2016*
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts