NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Naman layya tunda nama ne mai yawa kina da damar sarrafa shi yadda kike so. Ko dai ki soya shi ki ajiye shi a cikin kakide/kakile ko man kuli, ko kuma ki yi dambun nama da shi ko kuma ki yi kilishi da shi . Duk dai wanda kike so namanki ne sai ki sarrafa shi yadda kike so.

Assalamu alaikum, Uwargida barka da war haka, ya shirye-shiryen sallah? Da fatan Allah ya sa ayi sallah lafiya, aci nama lafiya ba tare da an yi zaryar zuwa asibiti ba ko kemis don bacin ciki. A ci nama baya-baya. Uwargida da fatan kin tanadi kasake da murahu da matsamai da manyan cokula don yin suyar nama. Idan baki da shi kuma to maza a tafi kasuwa a sayo miki domin suyar nama da yawa irin na sallah bata yiwuwa sai da wadannan kayayyakin aiki.
Uwargida idan da hali kada ki zauna ki ce sai Maigida ne kawai zai yi miki layya, idan da hali ke ma ki kwance kulli ki sayi rago domin yin layya. Kin ga kin sami rago biyu kenan. Domin yin layya abu ne mai kyau da muhimmanci ga lada. Kin ga rago daya sai ki yi sadaka da shi, dayan kuma sai ki soya shi ,ko ki sarrafa shi yadda ki ke so. Amma idan babu hali sai ki yanka na Maigidan kawai da ya kawo. Allah ya amfana, ka da ki zafafa, watarana Allah zai hore.
Naman layya tunda nama ne mai yawa kina da damar sarrafa shi yadda kike so. Ko dai ki soya shi ki ajiye shi a cikin kakide/kakile ko man kuli, ko kuma ki yi dambun nama da shi ko kuma ki yi kilishi da shi . Duk dai wanda kike so namanki ne sai ki sarrafa shi yadda kike so.
SUYAR NAMA
Idan an yanka rago ko sa, ko an soke rakumi ko kuma duk dabbar da Allah ya hore muku yankawa, sai ki fara da kayan ciki domin shi ake fara fitar wa. Ki wanke shi sosai, hanjin ki tabbata kin dura ruwa cikinsa, duk kazantar da take ciki ta fita. Sai ki zuba shi a cikin kasko, ki zuba gishiri da dunkulen knorr, ki yanka albasa da yawa ki zuba ruwa dai-dai kima ki rufe da babban murfi. Ki bar shi ya tafaso. Idan ya tafaso sai ki bude ki juya, idan kina so kina iya kara albasa saboda karni da ‘yar tafarnuwa. Haka zaki ringa yi har sai ya dahu. Idan ya dahu ba zaki bari ruwan ya kone kaf ba a jikin nama da dan sauran ruwa zaki saka mai domin suya. Idan da kakide/kikile wato kitsen da yake jikin ragon zaki yi suya sai ki yanka shi a kan kayan cikin. Idan kuma da man kuli zaki yi suyar sai ki zuba man kulin akan kayan cikin. Ki ringa yi kina juyawa har sai naman ko kayan cikin ya soyu. Sai ki kwashe ki zuba a cikin matsami ki bar shi domin man ya tsane sosai. Sai ki kawo barkono da citta da masoro da kika hada kika daka shi ki barbada shi a cikin naman ki juya sosai ko ina ya ji. Zaki yi hakan ne tun naman yana da zafi sosai domin ya shiga cikin naman sosai.
Wasu suna barin ragowar ragon sai a kafe shi ya kwana domin aiki yana yi musu yawa. A yayin da wasu kuma suke soya dukkan ragon a rana daya. Duk wanda Maigida yake so to haka zaku yi, sai dai ke idan kin ga aiki yayi miki yawa kina iya rokarsa arzikin a bar miki ragowar ragon sai washegari a sassara miki ki soya. To koma wanne kuka zaba duk daya ne. Yadda kika soya hanjin haka zaki soya ragowar naman, sai dai ki tabbata kin zuba albasa da yawa domin karni, kuma idan kin gama suyar ki barbada dakakken masoro da citta da barkono a cikin nama. Haka zalika kada ki soya nama da kashi lokaci daya. Ki soya su daban-daban ya fi sauki.
AJIYAR NAMA A CIKIN KAKIDE/KAKILE KO MAN KULI
Saboda yawan naman sallah, wasu su kan so su ajiye naman na wani lokaci mai tsawo. Kuma ajiyar nama na lokaci mai tsawo ba zai yuwu ba haka kawai musamman lokacin zafi. Saboda haka da akwai hanyoyi uku ko hudu da na san zaki iya ajiye namanki ya dan dade ba tare da ya lalace ba.
Ga hanyoyin kamar haka:-
1. Ajiya cikin man kuli:- kina iya ajiye namanki cikin man kuli ya dade miki sosai ba tare daya lalace ba. Idan kin gama soya namanki sai ki bari ya huce sosai. Ki soya man kulinki shi ma ki bari ya huce sosai. Sai ki kawo naman ki zuba shi a cikin wannan man kuli-kulin, amma ki tabbatar man kulin ya sha kan naman. Ma’ana man yafi naman yawa. Duk lokacin da kika tashi yin amfani da wannan naman sai ki saka cokali ki debo naman daga cikin man. Amfanin ajiya a cikin man shi ne yana saka naman ya yi laushi sosai , kuma dandanonsa baya canzawa.
2. Ajiya cikin kakide/kakile:- kakide/kakile shi ne kitsen da ake samu daga jikin rago. Wannan kakide/kakilen bayan kin gama suya sai ki zuba shi a cikin kwano ki bar shi ya huce sosai sannan ki zuba naman a ciki. Ki tabbata kakide/kakilen yafi naman yawa, wato ya rufe naman ruruf, domin koda nama guda daya ne ya fito bai shiga cikin kakide/kakilen ba to zai lalace, domin kuwa iska ce zata shiga ciki ta lalata naman da kakide/kakile gabadaya. Kin ga an yi biyu babu kenan. Sannan kuma ki tabbata duk abinda zaki zuba naman mai kakide/kakile a ciki kin zuba kakide/kakile ya kawo har bakin kwanon, domin kuwa idan kika zuba kamar rabi a cikin kwanon iska ce zata shiga ciki ta lalata shi. Nama a kakide/kakile baya fin wata uku ko hudu zaki ji dandanon sa ya sauya, ma’ana ba kamar yadda kika soya shi tun daga farko ba. Shi ya sa idan da hali da wadata ajiyar nama yafi a cikin man kuli. Kuma sannan idan lokacin sanyi ne duk lokacin da zaki yi amfani da naman sai kin dumama shi, sannan ki debi naman, wannan yakan sa naman ya ringa bushewa a hankali a hankali.
3. Busar da nama a rana:- wasu kuma sun fi son su busar da namansu a cikin rana, bayan an soya naman sai a ringa baza shi a rana har sai ya bushe. Duk lokacin da zaki yi amfani da shi sai ki watsa shi a cikin ruwan zafi domin ya yi laushi.
4. Ajiya a cikin firiza:- idan da hali da wadatar wutar nepa ko kuma inji, sai kawai ki sa a yanka-yanka miki namanki ki zuba a cikin leda. Duk lokacin da za ki yi girki sai kawai ki ciro shi daga cikin firiza ki dafa. Ko kuma kina iya dafa naman ki bari ya huce sannan ki zuba shi a cikin leda, duk lokacin da kika tashi amfani da shi sai ki ciro kawai.
Wannan hanya ma ita ce mafi sauki domin kuwa aiki da sallah yana yiwa mata yawa. Kuma idan kika saka a cikin firiza kin huta sayan nama na kwana biyu.
A sati mai zuwa in sha Allah zamu kawo muku yadda ake yin dambun nama da yadda ake ajiye kan rago ko sa, da kuma yadda ake yin farfesun kan rago. Ayi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana, ameen.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts