NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MAGANIN WARIN🙊 BAKI👄 KO TSAFTAR HAKORA😬 KO WARIN DA YAKE FITOWA DAGA MAKOGWARO (THROAT).

MAGANIN WARIN🙊 BAKI👄 KO TSAFTAR HAKORA😬 KO WARIN DA YAKE FITOWA DAGA MAKOGWARO (THROAT).

A nemi toka me tsafta a tankade ta, tokar asalin itacen da ake konawa a dafa abinci, sai kuma a nemi gawayi (Coal) na asalin itacen da aka kona, sai a daka gawayin ya yi gari sosai, sai Gishiri Dan kadan, sai a nemi ganyen Na'a-Na'a🍃 busashshe a daka shi ya dawo gari, sai a nemi lemon tsami me kyau nunanne🍋 a matse ruwan sa ta yadda ruwan lemon tsamin nan zai kwa6e hadin maganin gabadayansa. Sai a shanya ya bushe amma kar a tankade❌

Sai a nemi brush me kyau da dare in za a kwanta sai a yi brush a goge hakoran😬 da kan harshe👅 sosai, bayan an gama goge bakin sai a nemi ruwan khal tuffah a kurkure bakin da shi da ruwan zafi a hade. Haka za a dinga yi da dare in za a kwanta da kuma tsakar rana kaman 12 ko 1 na rana.

Wannan hadin yana gyara hakora yadda ya kamata, yana maganin Ciwon hakori😬 yana kara LAFIYAR hakora da jin dadin baki musamman ga ma'aurata, yana kuma cire tsatsar hakora😬
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts