NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

KALOLIN ALKUBUS DA YANDA AKEYI

ALKUBUS
• Alkama
• Fulawa
• Yist
• Kanwa
• Gishiri
• Mai
zaki tankade garin alkama da
fulawa ki hadasu waje daya ki
jika yis ki saka dan gishiri ki
kwaba yafi kwabin fanke tauri
ki rufe zuwa ya kumburo sai ki
dan disa mai da yar kanwa kiyi
ta bugawa ya bugu sai ki dauko
kana nan kwanuka ki shafa mai
a ciki ki zuba ki turarashi ko ki
zuba a leda ki kullashi kamar
alala ki dafashi,za a iyaci da
romo ko miyar taushe ko ta
agush.
note:zamu kawo muku yadda
akeyin na semovita wanda yafi
wannan ma sauki,mun gode.

Admin maijidda bello
Fatan alkairi ga masu Karatu ✍️

ALKUBUS DA MIYAR TAUSHE

KAYAN HADI:

FILAWA
YEAST
BAKING POWDER
GISHIRI

YADDA ZAKI HADA:

Ki tankade filawaki ki zuba baking powder kadan da gishiri shima kadan saiki jiqa yeast da ruwa ki zuba cikin filawa ki kwaba amma yafi kwabin fanke kauri, saikisa wuri mai zafi ko a rana ya tashi, saiki shafawa kofunan da zakiyi mai kisa ruwa a tukunya kadan saki jera kofunan ciki, Idan yayi ki kwashe sai ci.

MIYAR TAUSHE

ALAIYAHU
TATTASAI
TUMATUR
MAGGI
GYADA KO AGUSHI
MANJA
NAMA KO KIFI
TAGURU
ALBASA
GISHIRI

Ki blending tattasai tumatur albasa da taruru, ki wanke namanki ki zuba a tukunya ki yanka albasa kisa gishiri ki Dora tukunya a wuta, saiki yanke alaiyahunki ki wanke ki yanka masa albasa, saiki juye naman da kika Dora a roba, ki zuba manja ki yanka albasa, saiki cire namanki a ruwan tasafa ki zuba cikin manja kidan soya Sama Sama saki zuba kayan miyanki ki soya, idan suka soyu ki zuba ruwan tafasa nama ki qara da wasu kadan saiki rufe, ki tanadi maggin ki da gishi da agushi ko gyada ki zuba idan ta tafaso, idan ruwan miyan sunyi yadda kikeso kisa alaiyahunki ciki kibada minti 10 ki sauke Dan karya dafe yayi brown, saiki sauke kisa curry shike nan angama saki zubo alkubus sai ci.

Admin maijidda Bello ke gaishe da masu Karatu ✍️

Alkubus

flour 8 of milk tin

Yeast 1tablespn

mix ur flour with yeast and make a dough.

but d dough shouldn't be neither too thick nor too watery...

den cover and leave it to rest 4 abt 2-3hrs until double in size...

Apply little oil in tin or any container..sai ki zuzzuba nd steam it 4 10-15mnts..

idan yayi zaki ga ya ciccoko gwangwanin..datz all

ALKUBUS

Kayan hadi;

Alkama
Yeast
Mangyada
Ruwa

YADDA AKE HADAWA

Da fari dai zaki samu alkama mai kyau ki gyarata, ki bada akai miki nika ta zama gari.

Sai ki dauko garin alkamar ki samu mangyadarki kamar rabin gwangwami idan zakiyi kamar na tiya 1ne.

Sannan ki samu bowel mai tsafta ki zuba garin alkamar da yeast da mangyada da dan ruwa kadan, ki kwaba da dan tauri ba tikir ba amma yafi na funkaso tauri.

Sai ki rufe da murfi ta yanda iska ko kadan bazai shigaba, sai ki kaishi wajen rana ko waje mai dumi kibarshi yayi kamar 5hr.

Daga nan sai kisamu gwamgwamayen madara ko ledodi farare ki shafesu da mangyada kamar yadda ake shafa na gwangwanin alale.

Ki dauko kullin ki xuba gishiri dan kadan ki gaurayashi, sannan kina mulmulawa kina sawa acikin gwmgwmyen ko leda.

Idan kika gama zubawa sai ki dauko tukunyarki, kixuba ruwa dan kadan aciki, sai ki jera ledodin da kika zuba kullin alkubus din aciki .

Sai ki samu murfi ki rufe wadda bazai bar surace ya fitaba, kibarshi ya nuna, sai ki sauke.

Zaki iyaci da miyar TAUSHE KO EGUSHI

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts