NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

JIN ZAFI YAYIN SADUWA (jima'i)


FAMA DA JIN ZAFI YAYIN SADUWA (PAINFUL
INTERCOURSE)
Jin zafi yayin saduwa ababe daban daban
Kän jawo hakan kama da zafi daga waje-
waje farko farkon da azzakarin maigidan
ya fara shiga jikin macen.

💐💐💐SIRRIN YA MACE 💐💐💐

Wannan matsalar ta jin zafi har takansa Mace ta daina sha'awar sex din kwata-kwata🙅🏽‍♀

Kiga Mace gabanta yana fadúwa duk lokacin da Mijinta yake son suyi babbar ibadar aure (sex)


Meke Haddasa Matsalar Jin zafi lokacin da ake sex....?

Da Farko akwai Miji mai son kansa sosai, wanda baisan yayi wasa da matarsa ba yadda zai tsokano sha'awar matarsa kafin sex
To idan ya kasance kawai Miji hawan kawara zai yiwa matarsa gsky wannan yana Kawo mace ta kwaru ne kawai

Wato zai kasance Mace bata shirya ba kawai Miji zai hau....
Kuma ana yawan samun wannan matsalar
Lokacin da Mijin zai gama har ya Kawo ita kuma wata kila sai a lokacin ma zata dànyi sha'awa
To irin wannan Matar gaskiya bata more rayuwar aureIdan aka cigaba da har zata daina sha'awar sex kwata-kwata🙅🏽‍♀

*JIN ZAFIN JIMA'I DAGA MACE:*

A wasu lokuta ana samu mace tana jin zafi a yayin sex...

Kamar yadda mukace ta yiwu jin zafin yana faruwa ne saboda rashin sha'awar, mijin da macen keyi, sakamakon son kansa da yake wajen rashin tsokano mata da sha'awarta yadda zai tsaya suyi wasa sosai.

Ko kuma ya zama cewa wani ciwo ne da take dashi a gabobin sex dinta wanda yake kawo mata jin zafin.

Akwai matsalar ciwon Sanyi (infection) ds

A irin wannan hali ya kamata a shawarci doctor saboda cigaba da sex da wannan jin zafi yana sa mace ta rinka gudun sex dinJIN ZAFI A FARKO- FARKO
Shine fara jin tun kafin mutum ya gama
ratsa farjin mace sosai ya kai ga deep
penetrating.
Abunda Kän jawo irin wannan zafin akwai;
1- Rashin ni'ima ko ruwan farko farko mai
yauki dakan fara fitowa yayin da sha'awa
ta fara motsowa sosai. Abunda Kän jawo
rashin lubrication din bai wuce rashin fara
wasanni wato foreplay kafin fara saduwa.
2- Raguwar sinadarin oestrogen ajika ga
macen dake gab da daina haila, Rashin
jimawa da haihuwa ko shayarwa.
3-Akwai kuma nau'in magunguna da suma
Kän kai ga dauke damshi a farjin mace
wanda hakan kansa jin zafin irinsu
magungunan (hawan jini, nasa bacci, na
farfadiya, magungunan kawar da damuwa,
na allergies/mura, dana bada tazarar
haihuwa.
4- Jin rauni a farji Sakamakon tura yatsa
ciki ya zamto farcen mutum ya haifar da
rauni, ko wani abun daban kamar faruwar
hatsari, operation na kugu.
5- Kaciyar mata da akanyi nan ma ga macen
da akama irin wannan Kän fuskanci zafin,
ko Qari da akanyi ma mata yayin haihuwa,
ko shigar kwayoyin cuta Kän fatar farji, da
sauran nau'in cuttukan fata daka iya shafar
farji.
7- Ko mace ya zamto mai tsukakken gaba
yayin penetrating zata iya fuskantar zafi.
SAI KUMA ABABE DAKE SA JIN ZAFI DAGA CIKI
Wato zafi yada deep penetration. Wannan
Mafi yawa Kän faru ne Sakamakon wasu
cuttuka kamar;
1)- Cuttukan mara,
2)- Qarin cikin mahaifa (fibroid),
3)- Zazzagowar mahaifa (uterine prolapse),
4)- Canjin halittun cikin mahaifar mace,
5)- Ciwon mafitsara,
6)- Cutar basir,
7)- Karancin majinar cikin hanji dake tafiyar
da abunda ke ciki,
8)- Taruwar ruwa a kwan halitta (ovarian
cyst),
9)- Shigar kayan aikin likita jikin mace yayin
maganin Ciwon jeji wato radiotherapy and
chemotherapy.
SAI KUMA DALILI MAI ALAKA DA AIKIN
KWAKWALWA
A- FUSHI; wato kila sanda maigidan yazo ita
matar dama bataso wannan kanyi tasiri.
B- Damuwa ya zamto akwai wani Abu rai
ba abama saduwar cikakken attention ba.
C- Yanayin yadda mutum ya bayyana ga
macen wani yakan tsorata
D- Ko ya zamto dama ba wata jituwa
tsakaninku yanxu da taka ta taso kazo kana
lallashinta wannan kanyi tasiri gareta.
E- Idan ka zamto mai tumbi wato kugunka
bai zamto flat ba
F- Idan ya zamto antaba cin zarafin mace
wato kamar fyade ds.
MATAKAN DAUKA
1) Idan matsala ce ta ciwo ajikin macen to
aje ga likitocin mata azanta dasu adauki
mataki.
2) mata su jimanci tsarki da ruwan dumi,
3) Ga kowacce mace ta jimanci yin kigel
exercise wato ta intana zaune ko wanka
duk zata iya take sa hannu tana damke
gaban inta rike kamar secons 20 saita saki
haka zatake Yi safe yamma inta samu dama
akalla minti biyar biyar mai aure ko
budurwa.
5) Ga mazaje masu tumbi kuke kwanta su
matan suke zamtowa sune kanku.
6) Amfani da lubricant don samun santsi da
saukakawa.
Allah sa mudace, ya kara mana lfy tare da
zaunar da kasar mu lfy amin!
[Ibrahim y Yusuf
&
Maijidda Bello ✍️
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts