NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HAR YANZU BAMU DENA RASA RAYUKAN MATA MASU JUNA BIYU BA 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


HAR YANZU BAMU DENA RASA RAYUKAN MATA MASU JUNA BIYU BA
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Zuwa awon ciki ga mai juna biyu yana da matukar muhimmanci ga samun haihuwa lafiya cikin yardan Allah madaukakin Sarki.

Farkon abubuwan da ake yiwa ga sababbin zuwa, shine auna fitsari da jini don a tantance lafiyar mai ciki da nufin gano ko tana da wasu cutukan da zasu iya kawo mata matsala idan tazo haihuwa.
Misali ana gano alamomin ciwon kumburi da ciwon suga ta gwajin fitsari. Sanin kowa ne cewa ciwon kumburi ga mai juna biyu yana haddasa mutuwa in da karar-kwana. Ana kuma gano su ciwon sanyi da makamantansu.

A wajan gwada jini, ana gano alamun kwayar cutar HIV mai karya garkuwan jiki, ana gano adadin yawan jini a jikin mai juna biyu, domin karancinsa yana da illa.

Shi yake sa mai ciki ta rika fama da azababben ciwon kai, daga nan hawan jini ya bayyana a karshe kuma ya haddasa ciwon jijjiga ko tsikau-tsinkau a lokacin nakuda (pre eclampsia).

In ba'a je asibiti da wuri ba, ana iya rasa mai juna-biyu da jaririnta.

Da zarar an gano cutuka, ana baiwa mai lalurar magunguna don a warkar da cutukan da aka gano kafin lokacin haihuwa ta zo.

Misali masu hawan jini, ana basu magunguna tare da hana su cin gishiri, su kuma masu karancin jini, ana fada masu irin ganyayyakin da zasu rika ci masu kara jini, masu cutar HIV ko kanjamau, ana basu maganin da zai rage kaifin ciwon tare da wanda zai kare jaririn dake cikin mahaifa daga harbuwa da cutar HIV.

A wajan awon ciki, ana baiwa mata maganin rigakafin zazzabin cizon sauro wanda ke saurin hallaka mata masu juna biyu da jarirai 'yan kasa da shekara biyar (5) da haihuwa. Don haka, yaku dangi kada ashagala, mu tura matanmu da yayanmu zuwa awon ciki akan kari.

Ana fara zuwa awon ciki daga wata uku zuwa hudu idan an makara ke nan. Sau hudu kachal ake zuwa awo kafin haihuwa sai dai in akwai lalura mai karfi, ma'aikatan asibiti na iya fada wa mace lokacin da zata koma asibitin don a duba lafiyarta.

YADDA MAI JUNA BIYU ZATA RIKA ZAMA DA TASHI

Sanin kowa ne daga lokacin da ciki ya fara girma zama da tashi da kuma tafiya har da kwanciya kan zama wane kayan Gabas da ke bai wa mai juna biyu wahala, hakan yakan sanya rashin natsuwa da kwanciyar hankali ga mai juna biyu.

ZAMAN MAI JUNA BIYU

A lokacin da mai juna biyu za ta zauna, ya kamata ta zauna a kan duwawunta biyu, ma’ana ba a so ta rika bada karfi ko kuma zama a kan duwawu daya.

Sannan ya kamata ta zauna awajen zama da zai ba ta damar jingina ko kishingida, a lokaci guda bai kamata mai juna biyu ta zauna a wajen da yake da tauri ba, ma’ana wajen zaman da bashi da laushi ko kadan. Idan kuma kujerar da mai juna biyu take zaune bata da laushi, to za ta iya sanya karamin matashin kai, sannan ta jingina a kai.

TSAYUWAR MAI JUNA BIYU

Ba a so mai juna biyu ta dauki lokaci a tsaye. Yin hakan na sanya taruwar jini a kafafunta, wanda zai iya haifar da radadi a kafafun mai juna biyu, ko kuma ya sanya jiri ko hajijiya. Sannan dadewa a tsaye yana sanya wani nauyi a bayan mai juna biyu, ko ya haifar da ciwon baya.

Idan har ya zama dole mai juna biyu ta dade a tsaye, to ya kamata ta rika dora daya daga cikin kafafunta a kan karamar kujera, ko wani abu mai dan tsawo. Haka ya kamata mai juna biyu ta rika canza kafafunta a kan karamar kujerar, sannan kuma ya kamata ta rika hutawa lokaci zuwa lokaci. Kuma a duk lokacin da mai juna biyu za ta tsaya, to ta rika sanya takalma masu kyau, wadanda ba sa haifar da tara jini a kafafu.

Kota sanya wadansu takalma da ke yin tausa a kafafu wato ‘massaging shoe’, ko kuma ta rika daura ko sanya wani tufafi da ake kira ‘supporting hose’. Sannan idan mai juna biyu za ta daga wani abu, to abin ya zama kusa da jikinta, ma’ana kada ta bayar da tazara sosai tsakaninta da abin da za ta daga, domin yin hakan zai iya sanya nauyi ya rinjaye ta, wanda idan haka ta faru, zai iya haifar da wata matsala.

Ya kamata kuma mai juna biyu ta guji jujjuya jikinta a lokacin da za ta daga kaya.

Thanks 4 Ur time to Read it, Zanfi farin ciki inkukai aiki da ilimin FIYE da kui Like ko comments wallahi.

( Ibrahim Y. Yusuf )
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts