NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

AMOSANIN BAKI


Warin baki na nuni da wasu alamu da dama, duk lokacin da mutun ya fahimci bakin shi na wari, hakan na nuni da daya cikin biyu. Ko dai mutun baya wanke bakin shi a kai-a kai ko kuma mutun baya wanke bakin yadda ya kamata.

Rashin cin abinci masu gina jiki da cin abinci a lokacin da ya dace, na haddasa warin baki. Domin duk lokacin da bakin mutun, ya zamana yana da ragowar abinci, wannan lokacin ne wasu halittu a cikin bakin mutun zasu fara cin abinci, daga nan sai bakin mutun yayi karancin ruwa, miyau daga nan kuwa sai wari.

A duk lokacin da mutun ya ga cewar bakin shi yana wari kuma yana rama, to wannan alamu ne dake nuni da cewar mutun yaga likita. Haka idan bakin mutun ya faye wari, yana da kyau mutun yaje asibiti, don hakan yana faruwa idan mutun yana da matsala da kan iya shafar lafiyat hantar mutun.

Haka ma idan bakin mutun yana wari, kuma yana ganin wani farin abu a halcen shi, to shima alamu ne da yake nuna ma mutun cewar, yana dauke da wata cuta da take bukatar maganin cikin gaggawa.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts