NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YADDA ZAKIYI MANJA DAKANKIYADDA ZA KIYI MANJA DA KANKI

STEP 1: Za ki sayo kwakwar Manja, ki tabbata kin samo mai kyau mai kuma dadi',dan wata kwakwar bata da dadi shi yasa Idan tayi yawa a cikin kwakwa akayi Manja da ita sai ya riqa kama baki.

STEP 2:Ki jika ta cikin ruwa ta kwana, sai ki zuba ta a turbe ki sassafa ko ince ki surfa ta yadda bawon kwakwar zai rabu da kwallon.

A yayin da zaki fara dakan ki tabbata kin dora ruwa a wuta.

Idan ya tafasa sai ki juye cikin turmin da kwakwar take, ki motsa sosai sai ki juye ruwan cikin wata tukunya ki dora a wuta.

STEP 3:Idan ruwan kwakwar ya fara tafasa, za ki ga ruwan manjan na yo sama sai ki dinga yadewa kina zubawa a wata tukunyar har ya zama kin kwashe man.

STEP 4:Za ki kara dora wanda kika yade a wuta, shi Kuma zaita tafasa har sai ruwan ciki ya tsotse.

Daga nan sai ki sauke ki sami kwano ki juye manjan yadda zaki raba shi da duddugar da ke cikin tukunyar.

Shima Idan ya huce zai kwanta dattin ciki yayi kasa sai ki sami mazubi ki tsiyaye manjan.

Shikenan, ciki Lfy baka lafiya.

Mu sha ruwa
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts