NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YADDA AKE MAYAR DA MACE 'YAR LELE.
YADDA AKE MAYAR DA MATA 'YAR LELE.
Daure ka karanta.
Babu macen da ba ta son mijin ta ya rinka ji da ita, yana nuna mata soyayya da girmamawa. Yin haka na kara wa mace jin ta fi kowace mace ko jin ta a saman duniya, sannan duk yarintar mace ko tsufanta tana son mijinta ya rinka daukarta a matsayin ‘yar karamar yarinya wadda na taba bayani a kan hakan. Ma’ana ya rinka kula da ita kamar yadda zai kula da karamar yarinya, ya rinka tunawa da kuriciyarta da ya sani a da kafin ya aureta.
Saboda haka idan ba ka yin haka to daga yau ka fara don matarka ta rinka jin ita ma ta kai mace, ta samu farin ciki da jin dadin zaman aure. Na tabbata yin hakan na bayar da kwanciyar hankali a cikin gida, sannan na kara dankon soyayya sosai.
Rinka kula da irin sabon kayan da take sawa ko wani sabon abu da ta canja, kamar yin kitso, kunshi da kwalliya sai ka yaba da nuna birgewa a tare da kai. Duk wani sabon canji da ka gani yana da kyau ka san da shi, in na yabawa ne ka yaba in kuma na magana ne ka yi wannan shine zai kara tabbatar mata da kana damuwa da ita.
Kalmar yarinta kada ya rabu da bakin ka, kamar Bebita, ka rinka sawa tana jin a kullum ita ‘yar karamar yarinya ce a gurinka. Wani lokacin ma ka kirata da sunan da kasan babanta ko babarta suke kiranta da shi a lokacin da take karamar yarinya, sannan ka fada mata kalaman yabawa masu dadi da cewa tana da kyaun tsari.
Sai kira in ka fita office, ka kira matarka duk lokacin da ka kai office sai ka fada mata na kira ne don in tabbatar da jin lafiyar ki. Yin hakan nasa ta san tana da muhimmancin gaske a wurinka sosai.
Wata rana ka bata hutun shiga kitchen kamar ranar da babu aiki, sai ka shiga ka dafa abincin da za ku ci ko in ba zai yiwu ba sai ka fitar da iyalinka wani wurin birgewar da za su dade suna tunawa. Zuwa sayayya tare ko zuwa wurin hutu da shakatawa, ka rinka kukwa da ita kamar kwanan nan ka hadu da ita wato kamar wata sabuwar budurwarka.Kulawa ta musamman idan tana son yin magana da kai, ka juya ka saurareta da kyau in kana karatun jarida ko kallon talabijin sai ka rufe haka in an bugo waya kuna cikin tattaunawa kar ka dauka ko kuma ka kashe kafin ku fara tattaunawa, ka saurare ta da kunnen basira kamar yadda ka ke yi da in ka je zance. Sannan ka rinka nuna alamun kana ji da kyau ta alamun gida kai, murmishi ko amsawa. Sauraren abin da mace ka fada na daya daga cikin abin da ke sawa ta kara girmama ka.
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sawa ta dan huce ko ta samu sauki. Ka sa ta ji kamar ‘yar yarinya karama a kirjin ka. Ka bar ta har ta yi barci daga nan ne za ka gane irin baiwar da Allah ya yi mata da kyaun ta da kai kan ka baiwar da Allah ya baka.
Zama a gida ranar da babu aiki don kawai ka kasance tare da ita, sannan ta san kana tare da ita ne ba don kamai ba sai dan kana son ka zauna da ita, ka yi hira, wasanni, maganganun da za su sa ta ji dadin wannan kasancewar da kayi da ita, tunda nasha ganin matan dabasa son mijin su yana gida sai in lokacin da zai yi barci.
Yana da kyau wata rana ma ka kulleta a daki, don kar yara su dame ta sannan kar ka bar su su shiga har na kamar tsawon awa shida kawai don kana son ta yi barci ta huta, sai kai ka kula da yara na dan wannan lokacin, ka fahimtar da su cewa babar su na bukatar hutu bari ita ma ta dan ji dadin rayuwarta. Sai ka yi girki ka kai mata daki taci gaba da hutawar ta, babu abin da yake sa aji dadin soyayya face irin wadan nan abubuwan. Na san wani zai ce shi yaushe yake da lokacin hakan ko ya ce in ya yi haka ai ya bayar da kansa ga matar sa za ta raina shi. Wallahi babu maganar raini tunda wanda a kayi duniyar ma dominsa na tabbata kowa ya sami labarin irin wasan da yake da iyalin sa. Saboda haka ka zama miji nagari.
Bayan ka san ta sha gajiyar hayaniyar yara da aiki kitchen da daddare, sai ka sa ta kwanta don ka yi mata kyakkyawar tausa tun daga yatsu har zuwa kai, na tabbata za a ba ka kyautar da ba’a taba yi ma ba in dai har a ka ji dadin wannan tausa.
Sai bayan cin abincin dare, in an gama cin abincin dare da yara sai ka juya ka kalli yara ka yabi girkinta, sannan ka ce yaran duk su tashi su tafa wa babarsu, kuma su gode mata su gaya mata ‘Umma abincin ki ya yi dadi, gaskiya kin iya girki babu kamar yake.’ Sannan ka sa kowa ya rungume ta suna masu gode mata. Yana da kayu ka rinka yin haka lokaci lokaci.
Abin birgewa ne yadda wasu samarin suke kula da ‘yan matan su kafin aure, in aka lura da yadda wasu mazan suke yi da matan su na gida.
By maisana'a
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts