NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Yadda Ake Hada Man Karas Mai Kara Tsahon Gashi

Mutane da dama a shafukan yanar gizo sun gasgata ingancin wannan mai wajen kara tsaho da laushin gashi. Haka zalika za a iya shafa shi a jiki da daddare idan za a kwanta, wanda a nan ma yana taimakawa fata wajen kara laushi da rage alamun tsufa.

Ga abubuwan da ake bukata

Karas
Man zaitun ko man kwakwa
Fiya (Avocado Yadda ake hadawa

Da farko za a goga karas din da dan dama sannan a bare fiya guda daya a cire kwallon ciki.
A dora kasko a wuta, amma ba mai zafi ba sosai.
A zuba man kwakwa ko man zaitun din a cikin kwaskon, shima da dam dama
Sai a zuba karas da fiyan a cikin man a barshi ya soyu a cikin man
Ana yi ana juyawa a hankali
Ya kan dauki lokaci saboda wutar ba mai zafi ake bukata ba.
Idan ya soyu, sai a tace shi a bari ya huce.
A juye shi a cikin kwalba mai murfi.
Hanyoyin amfani da shi

Za a iya shafa shi kwana daya kafin ranar da za a wanke gashi. Idan aka shafa sai a rufe da leda a kwana da shi. Washegari sai a wanke gashin.
Za a iya amfani da shi a matsayin man kitso
Za a iya shafa shi a jiki da daddare a kwana da shi, da safe a wanke.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts