NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MAZA KU FAHIMCI WANANN


MAZA KU FAHIMCI WANNAN__
..
Namiji mai wasa da tsokana ya fi soyuwa a wurin mace fiye da namiji mai ɗaure fuska da rashin walwala.
Ko wane abu in ka duba akwai abun da yake ƙawata shi, to ni dai a ganina adon soyayya shine tsokana da wasa da dariya.
Domin yana sanyawa mace ta soyantu da namiji, da ya yi nesa da ita zata fara kewansa. Da ta masa wani abun da ya ɓata rai zata ji zafin itama a ranta.
Kuma kamar yanda zai rasa farin ciki ranar itama zata iya rasa nata.
Domin shine gishirin da yake bama gidan aurenta ɗanɗano. Wasa da tsokana a tsakanin ma'aurata yana sanya shaƙuwa, sabo, soyayya, nutsuwa da kuma farin ciki.
Kuma a kullum zasu rinƙa jin su tamkar basu girma ba, zai sa su rinƙa tunowa da lokutan su na daɗi da suka wuce.
Cunkusa fuska, da yin zumɓutu da kumatu bashi ne zai baka girma a gidanka ba.
Wai inda ya kamata a ce ka samu jin daɗi da farin ciki da walwala, nan ne kuma ka mayar da shi tamkar gidan maƙiyanka. Maza a gyara, a koyi salo, a koyi zama mai daɗi irin na Manzon Rahama (SAW). Saboda wasu ɗabi'unku shi ne zai sanyawa mata yi muku biyayya da rashin son su ga sun ɓata muku.
Domin duk mace mai hankali da tunani ba ta yin abun da zata ƙuntata ma mai son ta.
Mai kuma ƙoƙarin ganin gidan sa ya zame mata wurin farin ciki da annashuwa da gangar. In ku ka ƙuntata musu, ku ka hana su farin ciki to fa mace tamkar kunama ce, tana jin takura kaɗan zara fara harbi.
Iyaka dai ka san yanayin matarka da irin kalar tsokana da lokacin yin mata shi. Domin wasu matan akwai su da raini. Wata zata ɗauka wasan da kake mata kamar don baka san girmanka bane. Haka nan kema ki sashi ya soki ya shaku da ke ta hanyar tsokana.
Allah Ya baku ikon faranta mana, mu kuma Ya bamu ikon kyautata muku.
A yi soyayya a duniya a cigaba har a gidan wanzuwa.
..

Via:🖎Sadeeya Lawal Abubakar.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts