HEPATITIS
Hepatitis : Kamar yadda kowa yasani Hepatitis cutar hanta ce wacce take kunburar da hanta , kuma kwayar cutar virus ce take kawoshi .
A mafi yawan lokuta wadannan kwayoyin cutar virus suna zamansu ne kawai a cikin hanta ba sa kawo wata illa, sai dai ta Hepatitis B za ta iya kawo ciwon cancer.
HEPATITIS Ya kasu rukuni uku :
1- Hepatitis A
2- Hepatitis B
3- Hepatitis C
Wacce tafi addabar mutane a kasarmu Najeriya ?
Hepatitis B tafi addabar mutane a najeriya kamar yadda bincike yanuna .
Tayaya Mutun Zai Dauki wannan kwayar cutar Hepatitis B ?
Akoi Hanyoyi da dama ta yadda mutun zai iya daukan wannan cutar Hepatitis B . Ga kadan daga ciki :
1- Ana iya daukanshi ta hanyar jima'i da mai dauke da cutar .
2- Yaro zai iya dauka da uwarsa lokocin haihuwa .
3- Ana iya daukanshi lokocin karin Jini .
4- Ana iya Daukanshi daga kayan kaifi kamar su razor .
5- Ana lya daukan wannan cutan wajen amfani da syringe guda daya zuwa mutane diyawa .
Ance kwayar cutar Hepatitis B mutun zai iya daukanshi lokocin Gaisuwa ( shaking Hands )
Hmm Mutane suna fadan hakane dan sabida kwayar cutar Hepatitis B tana zama a Gumi , Yawu , Fitsari , Hawaye da Kashi kuma . shikenan suna nufin idan ka gaisa da mutun gumunku ya hadu kadauki Hepatitis B . to Bahaka bane .
Menene Halamomin Cutar Hepatitis B ??
Mafi yawa mutane suna dauke da wannan kwayar cutar amma basu san yana jikinsu ba sabida bata nuna wata halama ga wassu mutanen .
Amma ka kadan cikin halamominta :
1- Rashin cin abinci
2- Tashin zuciya
3- Amai
4- Rashin Karfin Jiki
5- Hajijiya
6- Ciwon Ciki
7- Ciwon Gabobi
8- Canxa kalar fata zuwa yellow
9- Canxa kalar ido zuwa yellow
10- wani lokocin da Zazzabi .
Amma idan kaga mutun yana fama da wadannan halamomin ba shi zai tabbatar maka da cewa yana dauke da kwayar cutar Hepatitis B ba . sai an gwada an tabbata .
Yaya Zan kare kaina Daga wannan cutar ??
Wannan cutar tana da rigakafi wanda ake kira Hepatitis B Vaccine .
Dakuma kiyaye wassu abubuwanda suke kawoshi a sama .
Menene Maganin wannan Cutar ???
Ba Hepatitis B kadai ba Duk wata cuta da kwayar cutar Virus take kawoshi bata da magani .
Amma banbancin Mutun mai dauke da Hepatitis B zai iya warke ko baisha magani ba yau da gobe kamar yadda mutun yakamu da mura yake warkewa .
Shikenan Babu wani magani da ake bawa mai fama da Hepatitis B ??
Hepatitis B ya kasu kashi biyu alal misali akoi :
1- Acute Hepatitis B : wannan Acute Hepatitis B tana nufin Hepatitis B wanda baiyi tsanani a jikin mutun ba . to shi wannan ba'a bada magani illa sai dai abashi shawarwari .
2- Chronic Hepatitis B : shi kuma wannan wanda yayi tsanani ne , shi ana iya bata Antiviral Drug's kamar yadda ake bawa masu cutar kanjamau .
To Lamivudine maganin menene ??
Yauwa kamar yadda nayi bayani a sama masu chronic Hepatitis B ana basu antiviral drugs kamar yadda ake bawa masu dauke da Ciwon HIV , to kaga wannan Lumivudine shima Antiviral drugs .
#Lafiya_uwar_Jiki