NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

DEWORMING TABLET Abune mai mahimmanci baiwa ya'yan mu da kannen mu kwayar maganin tsutsar ciki, micijin ciki da dattin ciki wato [ALBENDAZOLE] haka kuma wasu kan kirasa da ZENTEL.

DEWORMING TABLET

Abune mai mahimmanci baiwa ya'yan mu da kannen mu kwayar maganin tsutsar ciki, micijin ciki da dattin ciki wato [ALBENDAZOLE] haka kuma wasu kan kirasa da ZENTEL.

Lallai ka/ki ke ba yaranku duk bayan wata 3 saboda ya kashe kwayoyin worms din dana fada, Saboda suna dakile saurin girman yara gami da haifar ma yara karancin sinadarin "IRON" wanda ke Samar da wadataccen jini.

Wannan tasa wasu yaran ke tsumburewa alhalin suna da mugun cin abinci Amma kaga Basa Kumari, Saboda yara kan hadu da irin wannan kwayoyin Saboda wasan kasa, wasa da kwata, shan ruwan rafi, tare da cin abinci bayan tabe-tabe batare da hannu ya wanku ba.

YA MAGANIN YAKE?

Albendazole kanzo a 400MG duk kwaya daya a na roba kenan tsabarsa, haka kuma idan kwali ne yakan zo a 200MG Amma kwaya biyu ne a kwalin kunga ya tashi a 400MG.

ME ZAN KAUCEWA?

Maganin de anaso a tauna shi ahadiye ne Saboda baida daci, sai zaki zaki ma da yake dashi.

Ba'a ba yaro sai wanda ya shekara cif cif watanni (12)

Haka kuma mai juna biyu bata sha da mai shayarwa.

YADDA AKE

Idan shekarar yaro 1 zuwa 2 za a 6alla guda mai 400MG abashi rabi, kunga yasha 200MG kenan.
In kuwa dan kwali ne dama a 200MG yazo guda biyu kunga kai tsaye sai abashi guda daya ya tauna ya hadiye shikenan sai Kuma bayan wasu watanni ukun.

- Amma daga yan shekara 3 zuwa 12 za'a iya basu guda guda wato 400MG din duka su tauna su hadiye.

- Manyan kuma daga shekara 13 zuwa sama zasu iya shan kwaya biyu wato 800MG.

Sannan a Wadanda keda tsutsar cikin Akan bada shawara kafin kasha akalla da minti 15 ka sami ayaba ko gyada, ko kuli-kuli kaci inyaso bayan kamar minti 15 sai ka tauna maganin inka hadiye sai kabi da ruwa, hakan zai zamo kamar tarko inda maganin zai sami tsutsotsin guri guda ya kashe.

RASHIN BIN KA'IDA

Yana iya sa Yar gudawa kadan idan dadinsa yasa yaro ya haike masa yace zaita sha, musamman ace yasha kwaya 5 lokaci guda.

Amma baya kisa bakuma ya sanya Amai.

KU TAIMAKI YARANKU

Admin maijidda bello ✍️
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts