NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

CIWON SANYI NA MATA...... lalacewar farji
Admin maijidda bello

Ciwon sanyi mata wata babbar matsala ce sake addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da en mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata dayawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Shin menene ciwon sanyi? Meke kawo wannan cutar? Menene maganinta? Taya zan kare kaina daga kamuwa da ita? Domin samun amsoshin wanann tambayoyin ku cigaba da karatu...

Menene ciwon sanyin mata?

Ciwon sanyi, ko ace toilet infection ko vaginal infection dukka na nuni akan abu dayane. Ciwon sanyi wasu kwayoyin cuta ne dake addabar farjin mace. Wannan kwayoyin cutar na hana mace sukuni ta hanyar janyo kaikayin gaba, warin gaba, fesowar kuraje, fitowar ruwa faru ko yellow ko kore, jin zafi yayin jima'i, jin zafi yayin fitsari da sauransu.

Ire iren ciwon sanyi.

Ciwon sanyin dake damun mata bincike ya nuna kala kala ne. Amma zamu takaita akan guda 3 wanda sune sukafi cutar da mata.

1. Bacterial vaginosis

Wannan yana daya daga cikin manya manyan dake janyo wannan cutar. Acikin mata 100 dasukeda ciwon sanyi, kashi 50 suna dauke da bacterial vsginosis. Wannan na faruwa ne saboda yanayin canji na bacteria din dake jikin mace. Asali akwai bacteria masu bada kariya a farjin mace wanda ake kira da normal flora. Idan wanann bacteria suka habaka suka yadu sukan zama kwayoyin cuta kaman 'Gardnerella vaginalis' sai su haifar da ciwon sanyi.

Yaya ake kamuwa da wannan cutar?

Hanyoyin da ake kamuwa da wannan ciwon sanyi na bacterial vaginosis suke kamar haka,
1. Yanayin tsaftace farji
2. Amfani da abubuwan family planing kaman su implanon, intrauterine device (IUD).
3. Ciki
4. Mu'amala da maza dayawa

Alamomin Bacterial vaginosis
1. Jin zafi lokacin fitsari
2. Fitan farin ruwa mai karnin kifi musamman lokacin jima'i.
3. Fitan ruwa marar kauri sosai kaman kunu.
4. Kaikayin gaba.

Maganin Bactelrial Vaginosis
1. Metronidazole (Flagyl)
Idan kinada ciki daya haura wata 3 kada kiyi amfani da wannan maganin.
2. Clindamycin (cleacin)

2. Yeast Infection (Candidiasis)

Wannan kalan ciwon sanyin na faruwa ne sakamakon girman kwayoyin cutar 'fungus' wato Candida albicans a cikin farjin mace. Asali farjin mace na dauke da wannan kwayoyin halittar amma basa cutarwa har sai sun kara yawa. Suna kara yawa ne idan suka samu damshi, ko waje marar iska. Wannan kwayoyin cutar ba farji kadai suke tsayawa ba suna iya yaduwa a cikin jikin mutum. Mata da yawa suna kamuwa da wannan cutar a wani lokaci a rayuwarsu. A cikin kashi 100 kashi 75 sun kamu da shi. Cuta ce mai hatsarin gaske idan ba'a maganceta da wuri ba musamman ga masu ciki, ciwon suga ko kuma masu dauke da cuta mai karya garkuwan jiki wato HIV.
Amma ciwon sanyi na Yeast, ba ciwon da namiji sai iya dauka bane bayan jima'i duk da cewa bincike ya nuna a cikin kashi 15 cikin 100 na maza na samun kaikayin gaba ko fesowar kuraje bayan saduwa da macen dake dauke da wannan cutar.
Alamomin yeast infection
1. Kaikayin gaba
2. Radadi a farji
3. Fitan farin ruwa mai kauri, ko mai yanayi kamar awara.
4. Jin zafi yayin jima'i
5. Labben farji suyi jawur ko su kwaile
6. Fesowar kuraje.

Maganin yeast infection
Akwai magungunan da zaki sha domin magance wanann cutar...
1. Fluconazole (Diflucan) ko
2. Itraconazole (Sporanox)
Likita zai miki bayanin dosage din magungunan.
Sannan idan cutar bata fara karfi ba akwai wasu magungunan da xakiyi amfani dasu. Wannan sakawa a keyi a cikin farji, akwai vaginal tablets ko creams na kwana 7 zuwa 14 depending on yanda likita yace kiyi amfani dashi. Koda kin fara amfani dashi sai kikaji sauki bayan kwana 2 ko 3 kada ki dena amfani da shi ki cigaba har sai kin gama dose din sabado idan cutar bata mutu ba zata iya dawowa. Daga ciki akwai
Admin maij Bello


Nustatin (Mycostatin)
Miconazole
Clotrimazole ( wannan yafi karfi a cikinsu).

Yanada keu idan kina treating ciwon sanyi tuh idan da hali ki canxa wandunanki, idan babu hali ki wanke su dukka da ruwan dumi ki shanya a rana..

3. Trichomoniasis
Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa dashi ne ta hangar jima'i. Mata zata iya shafawa mijinta idan tana mu'amala da wasu mazan. Haka shima zai iya shafawa matar sa idan yanada mata sama da daya ko kuma idan yana neman mata.
Namiji ba kasaifai yake ganewa yanada wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayanna a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana ajikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana dashi.
Amma idan anyi sa'a ya bayannana cikin namiji akwai alamomi kaman haka;
Jin zafi wajen fitsari
Jin zafi bayan fitan maniyyi
Fitan farin ruwa kadan
Kaikayin gaba

Alamomin mata
Kaikayin gaba
Jin zafi wajen fitsari
Warin gaba
Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tass
Kwailewar farji

Yadda zaki magance wannan cutar
Metronidazole

Mata da maza duka zasu iya amfani da wannan maganain matukar suna dauke da cutar, kuma zasu kauracewa saduwa har sai sun warke.

Wasu alamomin ciwon sanyi
Ciwon mara Ciwon sanyi na janyo ciwon mara sosai koda ba lokacin ala'ada ba.
Wasa da al'ada Sai kiga ala'adrki na miki wasa, ko yanayin fitar jini ya karu .

Dabi'unmu na yau da kullum da zasu iya janyo wanann cutar na ciwon sanyi da rigakafinsu.

1. Yanayin tsaftace farji.
Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu, a ganinsu hakan shine dai dai. Kaman amfani da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami, medicated soaps da sauransu. Wanann ba tsaftaceki za suyi ba, hasalima kina kara bata halittar farjinki. Kaman yadda mukayi bayani a baya game da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wanannan hallitun na normal flora a cikin farjinki. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa, saboda haka er uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.

2. Yanayin wanke dubuwa bayan kinyi bayan gida.
Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gida shine ki fara daga gaba zuwa baya, ma'ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka sukeyi. Wannan dabi'ar sam bata dace ba. Idan kika fara daga baya kina debo kwayoyin cutar dake cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki. Hakan zai janyo miki da matsala babba. Shi farji baya san bakon abu a tattare dashi.

3. Amfani da bandaki mai datti
Yawancin mata na daukan ciwon sanyi bayan amfani da public toilets. Shiyasa ake cewa vaginal infection toilet infection.
Bandakin tsugunno: Idan misali mace mai wannan cutar tayi fitsari a kasa, sai kema kikaje kika tsugunna, fitsarinki ya taba wajen kuma ya dan fallatso a jikinki tuh fah er uwa zaki kamu da cutar. Saboda haka idan zaki tsugunnan ki tsugunna waje mai keu inda ba'ayi fitsari ba, kuma kiyi hankali kada ya fallatsa a jikinki.
Bandakin water system: kafin ki zauna kisaka tissue a cikin toitle sit din saboda farji a bude yake zai iya dauka kwayoyin cuta cikin sauki daga cikin toilet sit din. Kuma kada ki dade kina zaune akai.

4. Amfani da turare ko sabuku mai kamshi.
Dayawa mata na da wannan dabi'ar fesa abun kamshi ko wanke farji da sabulu mai kamshi. Wannan kusure ne babba, saboda su wannan kwayoyin cutar suna girma ne a inda yakeda damshi ko kamshi.

5. Amfani da jikakken wando.
Amfani da jikakken wando na haifar da cutar ciwon sanyi, saboda kaman yanda mukayi bayani a baya, kwayoyin cutar musaman na yeast na son waje mai damshi. Idan kin gama tsarki yanada mahimmanci daki tsantsane jikinki da towel mai keu kafin ki maida wandonki.
Kuma ki kasance kina amfani da wando da akayi da auduga (pure cotton) saboda sunfi tsotse damshi akasarin wanda akayi na nylon.
Sannan kindinga shanya wandunanki a rana saboda kashe kwayoyin bacteria akan shanya su a inuwa cikin bandaki.

6. Shan magani ba bisa ka'ida ba
Mutane nada wata dabi'ar sayan magani barkatai ba tareda sanin likita ba. Misali yawan shan antibiotics da kinga kurji a jikinki ko kina ciwon wuya da sauransu, na janyo infection. Bama vaginal infection kawai ba, hadda wasu cuttukan ma na daban. So a kiyaye yawan shan antibiotics batare da sanin likita ba.

6. Family planning
Idan mace na tsarin iyali domin samun tazarar haihuwa tuh akwai high chance din da xata iya kamuwa da ciwon sanyi. Saboda yanayin chanji na hormones dinta na affecting farjin mace. Koda kina shan pills, ko kinada implant a hannu , ko an daure bakin mahaifarki da dai sauransu.

Kuyi commenting a kasa, sannan kuyi sharing.


Admin maijidda bello
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts