NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YADDA MATAN GIDA ZASU YI AMFANI DA SPICES DA SEASONINGS

JIDDA'S KITCHEN🥘

YADDA MATAN GIDA ZASU YI AMFANI DA SPICES DA SEASONINGS

Kamar yadda muka sani ko wane spice da amfani shi kuma da dandanon shi. Akwai in da in saka wani zai ciwu akwai kuma wanda zai bata abun kika sashi shi a ciki.

A kullum mata maganar mu baya wuce na mazan ne basa bayar wa, duk da dai wani namijin yana badawa amma macen ne ba zata taba sakin jiki ta siya kayan ba, ta gunmace ta matse kudin ta, to amma in kika cire kudi kika siya ke kanki zaki jawo hankalin sa, in ba haka ba sai wacce kika fi komai tazo ta kwace miki miji da abinci, kuma in zaki duba zaki ga ba wani kashe kudi take yi ba, wata ma bata iya ba amma ta dauko hankalin sa da qamshin.

*Duk yanda zaki ji ance wani abu na da tsada to ana nan za a yi mai saukin kudin sa, sannan idan ma baki siya exactly irin waccen ba to ba za a rasa substitute nashi ba a kasuwa, don haka curry har na 30n akwai, haka ma thyme, su citta kuwa ko na nawa ne yan kasuwa zasu diba miki, to ke kuwa baki so ki wuce tsara? Ke kanki alfaharin ki ne qawarki, yanuwanki ko na mijinki su ci su yaba. Kin fi so ‘yayan ki su je unguwa suna yin wawason abincin wacce cefanenta bai kai na gidan ki ba? Kin fi so ‘yayanki su rinqa yaba abincin wasu ba naki ba? In kina yi musu mai dadi ba abincin ko wane gida ma zasu iya ci ba, sai su je unguwa suna fara ci su ajiye don sun san abincin maman su yafi. Don haka mu gyara mata.

* Misali: in zaki yi hadin spices na farfesu zaki iya hada: Garin citta, garin tafarnuwa, garin albasa, garin yaji, garin curry, thyme kadan, masoro da kanunfari paprika da basil saboda kin ga busassun ganye ne, sannan zaki iya saka cinnamon da habbatus sauda kadan sai ki hadasu wuri daya ya zama sune spices na farfesun ki. Kin hadasu kin ajiye, duk randa mai gida ya kawo dan kayan farfesun sa sai dai ki yi amfani dashi. Kada ki ce sai ya kawo ne sannan za a nema sai a rinqa samun matsala hajiya. Sannan sai ki duba maggin da ya kamata ki saka, da sauran seasonings masu qayata farfesu.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts