
Abubuwan da za a bukata Fulawa
•Suga
• ‘Baking powder’
•Butter/ man gyada
•kwai 15
Hadi:
Da farko dai, za a samu kwano ko roba sannan a fasa kwai guda goma sha biyar a ciki. Bayan haka sai a samu kofi tsaka-tsaki a auno suga daidai girman wannan kofi sannan a zuba a cikin ruwan kwan a yi ta gaurayawa har sai ta narke. A sake dauko wannan kofin da aka auna suga a narkar da ‘butter’ sannan a zuba a kofin har sai ya cika sannan a zuba a cikin hadin suga da kwai a cigaba da motsawa da muciya, sannan a debo ‘baking powder’ babban cokalin cin abinci daya ya cika sosai sannan a zuba. A cigaba da gaurayawa. A sake debo fulawa daidai cikin wannan kofin da aka auno suga da sauransu a auno fulawa kofi daya sannan a zuba a cikin hadin a cigaba da juyawa . Idan hadin ya yi ruwa-ruwa sai a dan kara fulawa kadan ta yadda in an sanya hannu ba zai manne ba. Amma kada a bar fulawar ta yi taurin hadin cincin din da aka saba.
A wanke hannu a goge sannan a gutsuro wannan kwabin a danna a tafin hannu a mulmula sannan a yi masa rami a tsakiya kamar awarwaron da yara mata ke sanya wa a hannu, sannan a dora man gyada a kan wuta a soya. A bar shi a kan wuta domin hadin ya soyu daga nan sai a soke.
Za a iya cin irin wannan cincin da shayi da kuma lokacin da za a tarbi baki.