NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HASKEN JIKIN MA'AIKI S.a.w...........oyoyo Ramadan

R

HASKEN JIKIN MA'AIKI (SAWW)

Kafiran Quraishawa sun bama Hassanu bn Thabit wata dukiya mai yawa domin biyan bukatarsu. Bukatar tasu ita ce wai suna so yazo ya kalli Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sannan ya Qirkiri wata waqar habaici game dashi.

Hassanu ya samu wani waje ya zauna yana jiran isowar Manzon Allah (saww) domin ya kalleshi ya samu abun fa'di. Amma yayin da Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yazo ya wuce ta gaban Hassanu ya ganshi, Sai ya tafi wajen Quraishawan nan ya mayar musu da dukiyarsu wacce suka bashi. Yace "Ga dukiyarku nan bana bukatar komai acikinta. Amma wannan da kuka bukaci inyi ma zambo, To ku shaida cewa hakika ni na Shaida cewa Shi Manzon Allah ne".

Sai suka ce "Menene ya tsorataka ne?. Ai ba don wannan muka aikeka ba".

Sai Hassanu basu amsa da baitukan yabo ga Ma'aiki (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa :

"Yayin da na hango haskensa yana Kyalkyali, Sai na sanya tafin hannuna akan idona saboda tsoro".

"Tsoro bisa idanuwana saboda kyawun siffarsa, ban isa kallonsa ba, sai dai bisa gwargwadon matsayina".

"Ruhi ne na haske acikin jiki Mai haske kamar farin wata. (Fatar jikinsa) Tamkar, kayan ado ne wanda aka saqashi da hasken taurarin nan na Zahra"

Ya Allah yi Salati da aminci bisa Shugabanmu, Annabinmu, Masoyinmu Muhammadu da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa gwargwadon girman matsayinsa awajenka. Ameen.

Albarkacin wannan salatin Ya Allah ka azurtamu da samun arzikin zama dashi da Makobtaka dashi acikin Aljannarka Firdausi mai daraja. Ameen.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts